Nasarallah; Iran Ce Zuciyar Al-Ummar Musulmi Kuma Cibiyar Gwagwarmaya.
Babban sakaren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sayyid Hassan Nasaralla ya bayyana cewa jumhuriyar musulunci ta Iran ce zuciyar al-ummar musulmi a duniya kuma ita ce cibiyar gwagwarmaya da maya-manyan azzaluman kasashen duniya.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Sayyid Nasarallah yana fadar haka ne a jawabin da ya gabatar a jiya Talata a birnin bayan jerin gwanon Ashura a duk fadin kasar.
A wani bangaren na jawabinsa shugaban kungiyar Hizbullah ya jinjinawa falasdinawa masu gwagwarmaya da haramtacciyar kasar Isra’ila da makamai, musamman kungiyar Jihadul Islami wacce ta kaddamat da shahidai a yakin kwanaki biyu da ta shiga da sojojin HKI a cikin wannan makon.
READ MORE : An Bukaci Gwamnatin Lebanon Ta Gaggauta Kammala Yerjeniyar Sayen Makamashi Daga Iran.
Daga karshe Sayyid Nasarallah y ace daga yanzu kungiyarsa ba zata taba amincewar kasar Lebanon ta rasa wani arzikin da All..ya huwace mata. Sannan ya ce yana hangen nasarori da dama nan gaba ga mutanen yankin gabasa ta tsakiya da kuma ga masu gwagwarmaya da azzalumai a kasashen yankin.
READ MORE : Sojojin Najeriya Sun Sake Kama Babban Dan Kungiyar ISWAP Wanda Ya Tsere Daga Kurkukun Kuje.
READ MORE : Iran; Cibiyar Sararin Samaniya Ta Karbi Sakonni Na Farko Daga Tauraron Dan’adam Mai Suna “Khayyam”.