Hukumomin Mali sun ce nakiyar da ake birnewa a gefen hanya ta halaka wani dan kasar Rasha da ke aikin taimakawa sojojin Mali wajen yaki da ‘yan ta’adda.
Wannan shi ne karo na farko da dan kasar Rasha dake aiki a karkashin kamfanin Wagner ya rasa ransa a kasar ta Mali.
Amurka, Faransa, da wasu hukumomin kasashen Turai jami’an da ake dauka a matsayin masu horas da sojojin Mali, jami’an tsaro ne daga kamfani mai zaman kansa na Rasha wato Wagner, said ai gwamnatin Mali mai rinjayen sojoji ta sha musanta wannan ikirari.
A wani labarin na daban Arsenal ta sake farfado da fatanta na kammala gasar Firimiya ta bana a tsakanin kungiyoyi hudu na farko , abinda zai ba ta damar halartar gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai ta badi, bayan doke Chelsea da kwallaye 4-2 har gida.
Nketiah mai shekaru 22 ne ya fara jefa kwallo a ragar Chelsea kafin daga bisani Timo Werner ya rama, Emile Smith Rowe ya sake ci wa Arsenal kwallo ta biyu, nan da nan kuma Cesar Azpilicueta ya sake ramawa Chelsea.
Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci ne kuma Nketiah ya sake cin kwallonsa ta biyu, ta amma ta uku ga Arsenal, sannan Bukayo Saka ya ci ta hudu.
Yanzu haka Arsenal tana matsayi na biyar a gasar Firimiya, bayan Tottenham ta hudu, dukkaninsu da 57-57, sai dai banbancin kwallaye, yayin da ya rage sauran wasanni shida a karkare kakar wasa ta bana.
A halin yanzu kuma maki 5 ne kawai tsakanin Arsenal da Chelsea wadad ke matsayi na uku da maki 62.
A wasu daga cikin wasannin da aka buga a jiya, Manchester City ta lallasa Brighton da kwallaye 3-0, an kuma tashi 1-1 tsakanin Everton da Leicester City.