Wani jami’in rundunar majalisar dinkin duniya ya mutu bayan da ya taka nakiya a arewacin Mali da ke fama da rikici a yau Lahadi, a yayin da yake sintiri a yankin, kamar yadda shugaban rundunar ta MINUSMA a Mali ya wallafa a shafinsa na Twitter.
Jami’in majalisar dinkin duniyar wanda yake daga cikin tawagar sojin kasar Guinea da ke aiki da dakaru na musamman ya ji rauni ne da farko, daga bisani ya mutu a asibiti a garin Kidal.
Wanann hatsari na zuwa ne a daidai lokacin da ake tattaunawa mai cike da tankiya a kan sabanta zaman rundunar ta MINUSMA a Mali.
Jimillar majalisar dinkin duniya na rundunar MINUSMA 175 ne suka mutu sakamkon rikicin da ake a Mali.
Rikicinn Mali ya yi sanadin mutuwar dubban daruruwan mutane, tare da daidaita da dama.
A wani labarin na daban kuma daga kasar amurka agajin garin birnin Uvalde a jihar Texas ta Amurka ya ce za a rushe makarantar nan da wani ɗan bindiga ya kashe yara 19 da malamai biyu a watan da ya wuce.
Don Mclaughlin ya sanar da hakan ne a wani taron hukumar birnin, inda mazauna birnin ke bukatar amsa a kan harin da aka kai makarantar.
Tun da farko wani jami’i a hukumar da ke kula da tabbatar da tsaron al’umma a Texas,Kanal Steve McCraw, ya shaida wa mahalarta taron cewa akwai kwakkwarar shaidar da ke nuna cewa jami’an tsaron da suka je wajen harin makarantar ba su yi abin da ya dace ba.
“Sun shafe fiye da awa ɗaya kafin su shiga ajin da aka kashe mutanen,” in ji shi.