Najeriya Zata Biya Miliyon $496 Ga Wani Kamfanin Kasar Indiya Dangane Da Kamfanin Karafa Ta Ajaokuta.
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta amince ta biya kamfanin ‘Global Steel group’ na kasar Indiya dalar Amurka miliyon $496 maimakon dala biliyon $5.258 da ya nema saboda soke kontragin da ta bawa kamfanin a shekara ta 2008.
Jaridar Premium times ta Najeriya ta nakalto Umar Gwandu kakakin ministan sharia Abubuakar Malami yana fadar haka. Ya kuma kara da cewa gwamnatin zata biya wadannan kudade ga kamfanin ne saboda bada kontragin da ta bashi a tsakain shekara ta 1999 zuwa 2007 na kula da kamfanin karafa ta Ajakuta.
Gwamnatin marigayi shugaba Ummaru Musa Yaraduwa ce ta soke kontragin bayan ta tabbatar da cewa bai da amfani ga kasar.
Sai dai masana sun bayyana cewa da gwamatin kasar ta saurar zuwa kwanaki 55 daga ranada ta soke kontragin ta sai dai kamfanin ya biya gwamnatin Najeriya dalar Amurka miliyon $26.
READ MORE : Iran Tana Iya Magance Karancin Makamashi A Turai Idan An Fahinci Juna A Tattaunawar Vienna.
Kamfanin kasar Rasha ne ya fara gina kamfanin karafa na Ajakuta da ke jihar Kogi, amma ba tare da kammala shi ba. Kuma da an kammala aikin gina kamfanin da zai zama cikin cibiyoyin fadada tattalin arzikin kasar mafi girma.