Najeriya Za Ta Sayi Jiragen Yaki Daga Kasar Amurka.
Amurka ta amince ta sayar wa Najeriya da jiragen soji masu saukar angula kirar Viper guda 12 a kan kudi kusan da bilyan daya, duk da kokarin da kungiyoyin kare hakkin dan adam suka yi domin ganin cewa Amurka ta hana wannan ciniki.
Gidan rediyon Faransa ya bayar da rahoton cewa, Sanarwar da Hukumar Hulda da kuma Tsaro da sauran kasashen duniya ta Amurka ta fitar, ta bayyana cewa wadannan jirage za su taimaka wa Najeriya domin tunkarar matsalar tsaro da take fama da ita, tare da taimaka wa sauran kasashen da ke yammacin Afirka ta fannin tsaro.
Yarjejeniyar cinikin Jiragen na AH-1Z Vipers mai dauke da tsarin hangen nesa ko cikin dare da kuma horo ya kai dalar Amurka miliyan 997.
Wannan na zuwa ne yayin da mahukuntan Najeriya suka bayyana fara amfani da jirage marasa matuka da aka fi sani da drones a wani yunkuri na kawo karshen ayyukan ta’addanci a Kasar.
READ MORE : Quds; Martani Kan Hare-Haren Isra’ila A Kan Masallacin Aqsa.
Mai taimaka wa shugaban Kasar ta fannin yada labarai, Malam Garba Shehu ne ya tabbatar da hakan, bayan ganawa ta musamman da shugaba Muhammadu Buhari ya yi da gwamnonin kasar 36 da kuma tsoffin shuwagabannin kasar.