Najeriya; Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Akalla 50 A Wani Coci A Jihar Ondo.
Mutane akalla 50 suka rasa rayukansu a yayinda wasu da dama suka ji rauni a lokacinda ‘yan bindiga suka bude wuta a ciki da wajen wani cocin Catholica a jihar Ondo na kudu maso yammacin Najeriya.
Shafin yanar gizo na labarai ‘Africanews’ ya nakalto wadanda suka ganewa idanunsu suna cewa wasu yan bindigan suna cikin cocin a lokacinda aka kammala adu’o’iin a Cocin ‘Ondo Diocese ‘ wasu kuma suna wajen cocin, inda suke bude wuta kan wadanda suke tserewa daga ciki.
Ba wanda ya dauki alhakin wadannan kashe-kashen. Labarin ya kara da cewa ‘yan bindigan sun yi amfani da nakiyoyi da kuma bindigogi masu karfi a kan mai uwa da wabi.
READ MORE : Iran Da Qatar Sun Rattaba Hannu Kan Yarjeniyoyin Raya Tattalin Arzikin Kasashen Biyu.
Sun kashe yara da manya da maza da mata. A arewacin Najeriya dai shekaru 13 kenan ana fama da yan bindiga na Boko Haram da masu riya kishin addinin da kuma yan fashi a duk fadin yankin, amma wannan shi ne karon farko da aka taba samun irin wannan mummunan kisa a kudancin kasar.
READ MORE : Iran Ta Sha Alwashin Ci Gaba Da Taimaka Wa Al’ummar Falastinu.