Najeriya Na Yunkurin Sasanta Ivory Coast Da Mali.
Wata tawagar da ministan harklokin wajen tarayyar Najeriya, Geoffroy Onyema, ke jagoranta ta gana da shugaban mulkin rikon kwaryar soji na Mali Kanal Asimi Goita.
M. Onyema, ya je a yunkurin sansanta Ivory Coast, da kasar Mali game da ragowar sojojin nan 46 da gwamnatin Bamako ke tsare da.
Saidai, a wata sanarwa da Malin ta fitar a jiya ta nuna cewa bai kamata Ivory Coast ta zama wata mafaka ta siyasa ga wasu jami’an Malin ba da kotun kasar ta fitar da sammacin kasa da kasa na neman su
Sanarwar da gwamnatin Mali, ta fitar ta zargi jami’an dake zaman mafaka a Ivory Coast da ‘yan neman tada zaune tsaye a kasar.
READ MORE : Iran Ta Caccaki Sabbin Takunkuman Amurka.
A ranar 10 ga watan Yulin da ya gabata Mali, ta saki uku daga cikin sojojin 49 da ta cafke bisa zarginsu da shiga kasar ba bisa ka’ida ba.
READ MORE : Aikin karamin ofishin jakadancin Iran a Karbala zai kasance awanni 24 a rana.
READ MORE : Elizabeth II: Shugaba A Afirka Ya Ayyana Zaman Makoki Na Kwana 3.
READ MORE : Yarima Charles, Ya Zama Sabon Sarkin Ingila.
READ MORE : Sojojin Isra’ila Sun Kashe Wani Matashi Musulmi Bafalestine.