Najeriya ba za ta yarda da duk wata shaidar karatu ba kan likitanci da ɗalibai suka samu daga jami’o’in Ukraine a shekarar 2022, a cewar Majalisar Likiitoci ta Najeriya ta Nigerian Medical and Dental Council (MDCN).
Majalisar wadda ke sa ido kan harkokin lafiya a Najeriya ta ce an ɗauki matakin ne saboda yaƙin da ake yi a ƙasar sakamakon hare-haren da Rasha ke kaiwa, abin da ya sa aka rufe azuzuwa na jami’o’i da manyan makarantun ƙasar.
“Muna sanar da jama’a cewa MDCN ba za ta yarda da shaidar karatun digiri ba kan harkokin lafiya da aka samo daga Ukraine a 2022 har sai harkokin karatu sun koma yadda aka saba,” in ji wata sanarwa da majalisar ta fitar a shafinta na Twitter.
Da yawa daga cikin jami’o’in na ci gaba da karatu ta intanet, matakin da MDCN ta ce ya saɓa wa manhajar koyar da likitanci.
“Domin kawar da shakku, majalisar na tabbatar da cewa duk wani horon likitanci da aka samu ta intanet ba mai karɓuwa ba ne kuma MDCN ba za ta amince da shi ba,” a cewar sanarwar.
Ita dai kasar Ukraine ta tsunduma yaki da rasha ne sakamakon kokarin shiga kungiyar tsaron NATO ta tayi rana tsaka wanda hakan ya zama silar fara wannan yaki kuma ya janyowa daliban dake karatu a Ukraine din matsala.
We wish to inform the General Public that Medical and Dental Degree Certificates issued by Medical Schools from Ukraine from 2022 will NOT be honoured by the Medical and Dental Council of Nigeria until when normal academic activities resume. 2/6
— Medical and Dental Council of Nigeria (@MDCNOfficial) June 17, 2022