Gwamnatin mulkin sojin Myanmar ta yi barazanar dakile huldar diflomasiya da Australia bayan da ta ce ba zata maye gurbin jakadiyarta da ta bar kasar ba.
Gwamnatocin yamma ne suka jagoranci caccakar da ake yi dangane da juyin mulkin da aka yiwa shugaba Aung San Suu Kyi na Myanmar din a shekarar da ta gabata.
A ranar Litinin ne kafafen yada labarai suka ruwaito cewa Australiya tace ba za ta maido da jakadiyarta da ta janye daga Myanmar ba bayan kammala wa’adinta, a maimakon haka, za ta nada wani jami’i da zai yi aiki a madadin jakada.
Mutane sama da dubu daya da dari 7 suka mutu
Kasar da ke kudu maso gabashin nahiyar Asiya ta fada cikin tashin hankali tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Fabrairun 2021, inda sama da mutane dubu 1 da dari 7 suka mutu sakamakon amfani da karfi fiye da kima da sojoji masu juyin mulkin suka yi, a cewar wata kungiyar da ke sa ido a kan batun da ya shafi hakkin dan adam a kasar.
A wani labarin na daban hukumar kula da zirga-zirgar jiragen kasa ta Najeriya NRC ta dage lokacin cigaba da jigilar fasinjoji a tsakanin Abuja zuwa Kaduna, sufurin da ta dakatar tun bayan harin da ‘yan bindiga suka kai kan daruruwan fasinjoji a ranar 28 ga watan Maris.
A baya dai hukumar ta NRC ta tsayar da ranar Litinin 23 ga watan Mayu ne domin cigaba da sufuri, amma ‘yan uwan wadanda ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da su suka ki amincewa da matakin, la’akari da cewar har yanzu ba a ceto ‘yan uwansu da aka yi garkuwa da su ba.
A wani mataki da wasu ke dangantawa da amsa bukatun masu koken ne kuma hukumar ta NRC ta hannun kakinta Mahmud Yakubu ta sanar da dage ci gaba da jigilar da ta shirya komawa, ba kuma tare da tsayar da sabuwar rana ba.
A baya bayan nan mataimaki na musamman ga shugaban Najeriya Muhammadu Buhari kan harkokin yada labarai Garba Shehu ya ce ana ci gaba da tattaunawa don ganin an sako mutanen da ‘yan bindiga suka sace a harin da suka kaiwa jirgin kasan da ke kan hanyar zuwa Kaduna daga Abuja.
Akalla mutane 9 aka tabbatar sun rasa rayukansu wasu sama da 20 kuma suka samu raunuka sakamakon harbin bindiga, sai kuma sace fasinjoji da dama a lokacin harin a watan Maris.