Mutumin da ya kwashe shekaru 30 yana rayuwa a cikin daji a Singapore.
Singapore na cikin kasashen duniya da suka fi yawan birane, inda ake ganin manya-manyan gine-gine da gidajen alfarma. Sai dai wani mutum ya zabi zama a wani gida da ya hada ta hanyar amfani da wasu itatuwa a tsakiyar daya daga cikin dazukan kasar.
Abin da ke soma jan hankalin mutum idan ya hadu da Oh Go Seng shi ne kyallin da ke idanunsa.
Bai yi kama da mai shekara 79 ba, domin kirar jikinsa ta sa ya fi wadanda ba su kai shi shekaru ba yaranta.
A farkon watan da muke ciki, labarin irin rayuwar da Mr Oh yake gudanarwa a cikin daji ta yadu a shafukan sada zumunta a Singapore – inda da dama daga cikin mutane suka nuna matukar kaduwa.
Wasu sun rika tambaya kan dalilan da suka sa ba a ba shi taimako sosai ba – sannan sun yi tambaya kan yadda ya shafe shekaru 30 yana rayuwa a cikin daji ba tare da an sani ba.
Rikici a lokacin bikin Kirsimeti
Al’amarin ya soma ne lokacin bikin Kirsimeti yayin da jami’ai suka tsayar da Mista Oh inda suka gano yana cinikayya ba tare da lasisi ba.
Yana sayar da ganyayyakin kayan miya da barkonon da ya shuka da kansa ne – bayan da annobar korona ta sa ya rasa aikinsa na sayar da furanni a kasuwani.
Mista Oh ya yi imani cewa wani abokin cinikinsa ne ya kai kararsa bayan sun sami wata takaddama kan dalar Singapore 1 da yake karba a matsayin kudin kayansa.
A wannan lokacin wani ma’aikacin bayar da agaji na wucewa, kuma ya lura jami’ai na magana da shi wadanda suka kwace masa kayan ganyen nasa.
Vivan Pan ta ce “ta fusata” a madadinsa, kuma ta ce: “Bana son ya koma gida ba tare da komai ba a wannan ranar.”
“Amma na fahimci cewa a karkashin dokar kasa, ba shi da izinin sayar da kaya a gefe tituna,” inji ta.
Sai ta dauki bidiyon al’amarin kuma ta wallafa shi a Facebook, inda ya yadu kamar wutar daji – kuma daga nan aka sanar da ani dan majalisar yankin halin da Mista Oh ke ciki.
Sai dai daga baya dan majalisar, Liang Eng Hwa y agano cewa akwai labaran abin mamaki dangane da rayuwar Mista Oh.
A zahiri ya shafe shekara 30 yana rayuwa ba tare da an san da zamansa ba.
Rayuwa cikin daji
Mista Oh y agirma tare da iyayensa a wani kauye mai suna Sungei Tengah.
Amma a shekarun 1980, an rusa wadannan kauyukan domin a gina wasu sababbin benaye.
Sai dai gwamnati ta ba yawancin mazauna kauyukan wasu sababbin gidaje, amma Mista Oh bai sami nasa ba.
Amma wani dan uwansa ya sami irin gidan na gwamnati kuma ya gayyaci Mista Oh ya zauna tare da shi – amma daga baya sai ya fice domin kamar yadda ya ce, baya son matsa ma iyalan dan uwan nasa.
Sai ya koma cikin daji kusa da inda tsohon gidansa da aka rushe ya ke, kuma ya rika kwana cikin wani wuri na wucin gadi da ya hada da katako da icen bamboo da kuma tarfo.
Idan ka isa matsugunin, za ka ga tokar da Mista Oh ke zubarwa bayan ya girka abinci. Akwai kuma tarin kayansa a tsakiyar matsugunin, kuma yana amfani da wani wuri a bayan matsugunin domin yin barci.
Akwai kuma wani wuri a kusa da matsugunin inda yake shuka abincin da yake ci. Ya kuma tsare ‘yar gonar tasa da igiya tsakanin bishiyoyin da wata danga.
Ya ce rayuwar kadaici a cikin dajin ba ta faye damunsa ba saboda ya kan mayar da dukkan hankalinsa kan ‘yar gonar da yake nomawa, kodayake ya ce wurin da gonar ta ke wuri mai albarka ne.
Amma ya ce abin da yafi damunsa shi ne beraye. Su kan kutsa cikin bukkar tasa har su kan rika cin kayan sawansa.
Ya kuma rika yin aikatau a duk lokacin da ya samu.
Mista Oh na amfani da kudin da ya samu domin ya biya kudin jirgin ruwa zuwa Batam, wani karamin tsibiri a kasar Indonisiya mai makwabtaka. A can ne ya ga wata mata mai suna Madam Tacih wadda ta haifar ma sa da ‘ya.
Sai dai bayan ziyarar da yake kai wa Batam, ya kan koma ‘gidansa’ na daji a Singapore.
Kamar sauran ‘yan uwansa, matar Mista Oh da ‘yar tasa – wadda yanzu shekarunta na haihuwa 17 – sun ce ba su san cewa a daji yake zama ba.
“Ya kan ce a wani gandu nake zama”, inji wani dan uwansa.
Bayan da annobar korona ta bayyana, Mista Oh ya daina tafiya Batam, sai dai ya ci gaba da aika wa iyalansa dala 500 zuwa dala 600 na kudin Singapore a kowane wata.
‘Na kalli talabijin a karon farko’
A watan Fabrairun wannan shekarar – ranar farko ta sabuwar shekarar da ‘yan Singapore ke amfani da ita, wata tawagar dan majalisar mazabar Mista Oh sun ba shi sabon gida.
Dan majalisa Liang ya ce shi da tawagar tasa za su ci gaba da taimaka ma Mista Oh, ciki har da hada shi da matarsa da ‘yarsa da ke Indonisiya domin su zauna wuri guda.
Sabon gidan nasa gida ne mai dakin kwana daya, wanda yake zama a ciki tare da wani mutum, sai dai dan karamin gida ne kuma babu kayan more rayuwa sosai a cikinsa.
Baya ga ‘yan kayansa, akwai firji domin sanyaya ruwa da talabijin da butar dafa shayi da na’urar dafa shayi – wadanda duka abokan arziki ne suka ba shi.
Mista Oh ya yaba da na’urar dafa shayin. Ya saba da wanke kayansa a wani tafki kusa da matsuguninsa na da, kuma ya ce ruwan famfon sabon gidan nasa ya faye sanyi.
A yanzu yana tukin mota ne, inda yake dakon ma’aikata ‘yan kasar waje daga wajen aiki daya zuwa wani wajen aikin, kuma a wani jikon yana yin aikin gona, kamar yadda ya ce.
Ranar da ya koma sabon gidansa ce ranar da ya yi biki shigowar sabuwar shekara tare da iyalansa cikin shekara 30.
Ya ce, “na ci abinci sosai! Kuma na ci wasu nau’in abincin da na dade ba ci ba!”
“Abin jin dadi ne. Na kuma kalli talabijin a karon farko cikin shekara fiye da talatin. Na ji dadin yin haka sosai.”
Sai dai duk da wannan ci gaban ya ce yana kewar ‘yancin rayuwar da yayi ta cikin daji, kodayake ya ce ya fi son rayuwa a cikin sabon gidan nasa.
“Na rayu a daji na shekaru masu yawa, saboda haka lallai ina kewar wurin sosai,” inji shi. Ya bayyana haka ne cikin harshen Hokkien, wanda ke cikin harsunan kasar China.
“Ko yanzu na kan shiga dajin a kowace rana. Na kan farka da kamar karfe 3 a dare, sai in sanya tufafina kuma in tafi dajin domin duba gonar kayan miyar da na shuka, kuma na kan yi wannan aikin ne kafin in fara ayyukan da nake yi na tuki.