Mutum shida sun jikkata a harin tashar jirgin ƙasa a birnin Paris
Hukumomi a birnin a ƙasar Faransa sun ce wani mahari ya soki mutum shida da wani makami a tashar jirgin ƙasa ta birnin Paris da ke ƙasar Faransa, kafin daga bi-sani ‘yan sanda su harbi shi tare da kama shi.
Tashar jirgin ƙasan mai cike da cunkoson mutane ta kasance babbar tashar jiragen ƙasa da ke zirga-zirga zuwa arewacin Faransa da Landan da kuma arewacin Turai.
Jami’an ‘yan sanda na ɗaukar suka da wuƙa a matsayin yunƙurin kisan kai, a maimakon harin ta’addanci, kamar yadda wata majiya ta bayyana.
Kawo yanzu dai ba a san manufar maharin ba.
”Ɗaya daga cikin mutum shidan da maharin ya soka na cikin matsanancin hali, yayin da sauran biyar ɗin suka samu ƙananan raunuka”, kamar yadda mai shigar da ƙara ya bayyana.
Ministan cikin gida na ƙasar ya shaida wa manema labarai cewa ”duka duka lamarin ya auku ne cikin mintuna biyu”.
Kawo yanzu ba a san wane irin makami maharin ya yi amfani da shi ba.
Da fari ‘yan sanda sun ce wuƙa ce, sai dai daga bi-sani ministan cikin gidan ya ce ba wuƙa ba ce, wani mummunan makami ne.