Mutum Guda Ya Mutu Sa’ilin Zanga Zangar Nuna Kin Jinin Gwamnati A Kasar Sudan.
Jami’an tsaro sun bude wuta kan masu zanga-zangar kin jinin Gwamnati a Omdurman da birnin Khartum kuma yayi sanadiyar mutuwar mutum Guda, lamarin da ya kara fantsama zanga-zangar a sauran sasssan kasar .
Wannan shi ne ya cika adadin mutane 116 ke nan da sojojin suka kashe a kokarin da suka yi na murkushe masu zanga-zangar nuna kin jinin juyin mulkin da sojoji suka yi karkashin jagorancin kwamandan hafsoshin sojin kasar Abdel Fatah Al’burhan
Kungiyar neman canji da yanci na kasar Sudan ta yi kira ga alummar kasar da su gudanar da gagarumar zanga-zanga a fadin kasar, idan a birnin khartum masu zanga-zangar sun rika data tutar kasar suna kuma rera taken cewa Sudan kasa ce ta kowa da kowa , babu kabilanci babu banbanci.
READ MORE : Kasar Turkiya Ta Sake Kai Wani Sabon Hari A Arewacin Kasar Iraqi.
Kasar Sudan ta fada cikin rikici ne tun bayan da sojojin suka kwace madafun iko karkashin jagorancin al-burhan a watan Oktoban shekara ta 2021 bayan da suka kama fira ministan kasar Abadallah Hamdok da wasu shugabanin fararen hula.
READ MORE : Rashin Tabukawar Kwamitin Tsaro Na Karawa Isra’ila Karfin Guiwar Ci Gaba Da Zaluntar Falasdinawa.