Dubban mutane sun tsere daga gidajensu a yammacin kasar Myanmar, biyo bayan kazamin fadan da aka kwashe kwanaki ana gwabzawa, tsakanin dakarun kasar da mayakan sa kan da suka yi wa sojojin da suka yi juyin mulki tawaye.
A baya bayan nan ne kuma, hare-hare kan dakarun na Myanmar suka karu, tun bayan da a farkon wannan wata na Satumba, ‘yan majalisun dokokin da gwamnatin sojin kasar ta tsige suka yi kira da daukaci al’ummar kasar da su fito kwansu da kwarkwatar su domin yin juyin juya halin da zai kawar da sojojin.
Tashin hankali na baya bayan nan da ya tagayyara dubban mutane shi ne kazamin fadan da aka gwabza tsakanin sojojin na Myanmar da ‘yan tawaye kimanin 100 da suka yi wa dakarun kwanton Bauna a yankin Thantlang da ke jihar Chin a kusa da iyaka da kasar India, ranar 18 ga watan Satumba.
Kungiyoyin fararen hula da ke bibiyar lamurra a Myanmar sun ce fararen hula fiye da dubu 1 da 100 aka kashe, yayin da kuma jami’an tsaro suka kame wasu kusan dubu 8, tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Fabararairu.