Bayanai suna ci gaba da kara fitowa dangane da harin da aka kai a birnin Kabul na kasar Afghanistan, inda rahotanni da suke fitowa daga kasar suka tabbatar da cewa mutane dari da uku ne suka rasa rayukansu a tagwayen hare haren da kungiyar Daesh ta dauki alhakin kai wa a birnin na Kabul babban birnin kasar a jiya Alhamis, jama’a dai na cigaba da bayyana ra’ayoyin su dangane da lamarin
Daga cikin wadanda suka rasa rayukan nasu har da sojojin Amurka goma sha uku wadanda aka tabbatar da cewa sun mutu, sai kuma fararen hula akasari mata da yara.
Shugaban Amurka Joe Biden ya sha alwashin farautar wadanda suka kai hare-haren na Kabul, yana cewa za su dandana kudarsu.
Ya kuma ce za a ci gaba da aikin kwashe mutanen da ake yi, duk da barazanar maharan.
An dai bayyana harin da mafi muni ga sojojin Amurka a Afghanistan, tun daga shekarar 2011.
Kawo yanzu dai sama da mutane dubu dari ne aka kwashe daga kasar ta Afghanistan tun bayan da kungiyar Taliban ta kwace mulki.
A nata bangaren Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi Allah wadai da hare-haren ta’addancin da aka kai ranar Alhamis a Kabul, ciki har da filin jirgin saman birnin.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Saeed Khatibzadeh, ya yi tir da kakkausar murya da tagwayen hare -haren ta’addanci da aka kai a Kabul, ciki har da tashin bam a filin jirgin saman Kabul.
Haka nan kuma ya bayyana fatan cewa za a kafa gwamnati mai cikakken iko a Kabul cikin gajeren lokaci.
Gwamnatin kasar Iran ta yi fatan hukumomin da abin ya shafa zasu dauki nauyin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.