Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa, yankin Tillaberi na yammacin Jamhuriyar Nijar na fuskantar babbar matsalar abinci, inda kusan mutane dubu 600 ke fama da matsalar karancin abinci.
Ofishin Kula da Ayyukan Jin-Kai na Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadin cewa, rashin tsaro da hare-haren da ake zargin wasu kungiyoyin masu dauke da makamai da ke kai hari ga manoma da fararen hula za su haifar da mummunan sakamako a wannan shekarar kan halin rashin abinci.
Yankin na Tillaberi da ya kai girman Koriya ta Kudu ko Hungary, na da iyaka da kasashen Burkina Faso da Mali da Benin.
Majalisar Dinkin Duniya ta kuma yi gargadin halin da ake ciki a sashin Banibangou zuwa arewa maso gabashin Tillaberi, inda ake sa ran sama da mutane dubu 79 za su su fuskanci tsananin yunwa.
Tsakanin watan Yuni da Agustan shekarar da muke ciki, wani gungun ‘yan bindiga ya kashe mutane da dama a Banibangou a cikin gonakinsu, wanda hakan ya tilasta wa jama’a yin watsi da gonakinsu.
A wani labarin na daban kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International ta ce hare-haren kungiyoyi masu ikirarin jihadi sun tsananta cikin shekarar nan a Jamhuriyyar Nijar inda galibi maharan a yanzu kan mayar da hankali kan kananan yara.
Amnesty ta bayyana cewa kananan yara fiye da 60 suka rasa rayukansu a hare-haren kungiyoyin ta’addanci da ke ikirarin jihadi a kasar ta Nijar cikin shekarar nan.
Alkaluman da rahoton ke dauke da shi ya nuna yadda fararen hula fiye da 500 suka rasa rayukansu a hare-haren ‘yan ta’addan daga watan Janairu zuwa Yulin shekarar nan.
Amnesty ta ce Alkaluman mutane da hare-haren kan kashe ya karu a bana idan aka kwatanta da mutum 397 da suka mutu a bara.
Kungiyar ta Amnesty International ta kuma ja hankali kan yadda wata kungiyar ‘yan ta’addan da ke da alaka da al-Qaeda ke yaudarar kananun yara da shekarunsu ya fara daga 15 zuwa 17 wajen shigar da su ayyukan ta’addanci.
A cewar Amnesty kungiyar kan ci ribar halin tsananin yunwa da kulle makarantun da yanzu haka yankin na Tillaberri ke ciki, inda ta ke baiwa yaran abinci ko wasu abubuwan more rayuwa tare da ribatarsu cikin ayyukan ta’addanci.