Rahotanni sun ce mutane masu zanga zangar na daga cikin magoya bayan sojojin da suka gudanar da juyin mulki a kasar ne.
Sai dai duk da gargadin na Faransa alamu na nuna cewa Sojin na Mali na shirin kawar da kai wajen dakko sojojin hayar na kamfanin Wagner daga Rasha don taimaka mata a yaki da ‘yan ta’addan da suka addabi kasar.
Sojin hayar na Wagner dai sun taimaka a yakin kasashe irinsu Syria da Libya yayinda yanzu haka suke taimakawa a yakin da jamhuriyyar Afrika ta tsakiya ke yi da ‘yan tawaye.
A wani labarin na daban daruruwan mutane sun yi zanga -zanga a Bamako babban birnin Mali, inda suka bukaci a ba wa shugabannin sojan kasar karin lokaci don tsara zaben da zai sake mayar da mulki ga farar hula.
Bayan juyin mulkin da sojoji suka yi wa tsohon shugaban Mali Ibrahim Boubacar Keita a watan Agustan shekarar 2020, sun nada gwamnatin farar hula ta wucin gadi da aka dorawa alhakin mayar da kasar kan mulkin dimokaradiyya.
Sai dai a watan Mayu sojojin a karkashin Kanal Assimi Goita suka sake kwace mulki gami da ayyana shi a matsayin shugaban rikon kwarya.
Goita ya yi alkawarin mutunta wa’adin na shirya zaben na watan Fabrairu, to amma wasu na shakku game da hakan.