Mutane 60 Ne Suka Mutu Sanadiyar Fashewar Wani Abu A Wajen Hakar Ma’adinai A Burkina Faso.
Majiyar labaran Asibiti a a kasar ta sanar da mutuwar akalla mutane 60 tare da jikkatar wasu da dama sakamakon fashewar wani abu mai kara a wajen hakar ma’adinai na zinariya ba bisa ka’ida a Arewa maso Gabashin kasar Burkina Faso.
Hotunan video da aka nuna yadda fashewar ta Afku ya nuna yadda bishiyoyi da dama suka fafi tare da rusa gidaje , inda aka ga gawawwakin mutane da dama kwance a yaje a kasa,
Majiyar Asibitin ta kara da cewa Adadin wadanda ke mutuwa din yana iya kara karuwa bisa la’akari da halin rai kwakwai musu kwakwai da wasu marasa lafiyan ke ciki, Mata da yara kanana na daga cikin wanda abin ya ritsa da su,
Kasar Burkina faso tana daga cikin yankuna masu arzikin Ma’adinai na zinariya da wasu kamfannonin kasashen waje suka mayar da shi a matsayin gida , sai dai akwai kana nan wurare sama da da 100 da ake ayyukan hako zinariya ba bisa Kai’da ba a kasar
Kasar na fuskantar hare-hare kungiyoyi masu Ikirarin Jihadi dake da alaka da kungiyar Al’qaida da Daesh da suke kokari karbe ikon wuraren da ake hakar zinariya don su rika amfani da su wajen kai hare-hare.