Ana fargabar cewar akalla mutane sama da 100 suka mutu sakamakon wata gobarar da ta tashi a wajen tace danyan man fetur ba bisa ka’ida ba akan iyakokin Jihohin Imo da Rivers da ke Najeriya.
Sai dai mai magana da yawun ‘Yan Sandan Jihar Rivers Grace Iringe-Koko tace yankin ba a cikin Jihar Rivers yake ba, inda ta kara da cewar yana Jihar Imo ne.
Jaridar tace Fyneface wanda ya gabatar mata da wasu hotunan hadarin da babu kyaun gani, yace bayan mutanen da suka kone kurmus, wasu motocin da suke dakon a zuba musu man satar suma sun kone kurmus.
Ko a makon jiya sanda aka samu irin wannan hadari a karamar hukumar Rumuekpe Emohua inda mutane sama 30 suka mutu cikin su harda yara, abinda gwamnatin Jihar Rivers ta danganta shi da fashewaer gas da satar man.
Jihohin Rivers da Imo na daga cikin wadanda ke fama da matsalar fasa bututun mai ana sata da kuma masu tace man a haramtattun matata.
A farkon shekarar nan Gwamnan Jihar Rivers Nyesom Wike ya kaddamar da samame akan barayin man da zummar dakile ayyukan su saboda abinda ya kira zagon kasa da matakin nasu ke yiwa tattalin arzikin Najeriya.
A wani labarin na daban Hukumomin Mali sun ce nakiyar da ake birnewa a gefen hanya ta halaka wani dan kasar Rasha da ke aikin taimakawa sojojin Mali wajen yaki da ‘yan ta’adda.
Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ce tawagar sojin Mali da ke dauke da dan kasar Rashar ta taka nakiyar a kusa da garin Hombori, kuma kafin akai shi birnin Sevare ta jirgin sama ya mutu.
Wannan shi ne karo na farko da dan kasar Rasha dake aiki a karkashin kamfanin Wagner ya rasa ransa a kasar ta Mali.
Amurka, Faransa, da wasu hukumomin kasashen Turai jami’an da ake dauka a matsayin masu horas da sojojin Mali, jami’an tsaro ne daga kamfani mai zaman kansa na Rasha wato Wagner, said ai gwamnatin Mali mai rinjayen sojoji ta sha musanta wannan ikirari.