Miliyoyin musulmin duniya ne suka fito titunan biranen su a Juma’ar karshen watan ramadana domin nunawa duniya cewa suna tare da al’ummar Palestine dangane da zaluncin da isra’ila take musu.
A shekarar 1979 ne dai jagoran juyin juya halin musulunci na Iran, Ruhulla Khumaini ya ayyana juma’ar karshen ramadana a matsayin ranar nuna goyon baya ga musulmin Palestine domin raya lamarin falasdinawa a duniyar musulmi.
Mutane da dama ne suke shiga wannan kamfe kowacce shekara a fadin duniya.
A Najeriya wannan kamfe na Palestine ya karkasre da zubar jini a lokacin da ‘yan sanda suka bude wuta kuma suka kashe daya gami da raunata da dama, kamar yadda kafar sadarwa ta Press T.v ta rawaito.
Daya daga cikin wadanda suka ji rauni an harbe shi a kirji, yayin da sauran aka harbe su a kafa, an ruga da wadanda suka ji raunuka zuwa asibiti.
Bidiyoyi daga Abujan sun nuna ‘yan sanda suka harba barkonon tsohuwa yayin da mutane ke kokarin neman kariya.
A Kaduna ma shaidar gani da ido ya tabbatar da cewa, ya ga ‘yan sanda suna harbin ‘yan uwa musulmin masu ralin goyon bayana Palestine yayin da suke kokarin neman kariya.
Sai dai har yanzu babu labarin samun masu rauni daga Kadunan.
Wannna gangami dai anayin sa ne duk juma’ar karshen watan ramadana mai alfarma domin samar da dama ga masu neman ‘yanci na duniya ba tare da lura da addini, launin fata ko bangare ba su bayyanar da goyon bayan su raunanan Falasdinawa, sa’annana su bayyana fushin su dangane da ayyukan zaluncin gwamnatin isra’ila.
A sauran garuruwan Najeriya ma irin su Kano, Katsina, Postiskum da sauran su ma an gudanar wadannan muzaharori na lumana domin goyon bayana al’ummar Palestine kamar yadda aka saba gudanarwa duk shekara.
Kasashen makota ma irin su Nijar ba’a barsu a baya ba domin sun gudanar irin tarukan na goyon bayan Palestine.