‘Yan uwa musulmi almajiran Malam Zakzaky ne sukayi gangamin domin nuna rashin goyon bayan su ga kisa gami da azabtarwar da akewa ‘yan shi’a na kungiyar hadin kai dake Azrbeijan (MMU) tare da jagoran su Sheikh Haj Taleh Baqir Zadeh.
Gangamin wanda ak gudanar a babban masallacin juma’a dake Abuja ranar asabar ya samu halartar Abdullahi Musa, sakataren bangaren dalibai na harkar musulunci a Najeriya (Academic Forum).
An jiyo musa yana mai cewa, “Gwamnatin Azarbeijan tana azabtarwa gami datakura musu”
“Saboda hakanan kowanne musulmi dole ne ya tsaya domin taimakon musulmi’
Matasa masu wanann gangami sun hau kan titi suna kwala kalmomin “Mutuwa ga Amerika’ Mutuwa ga Isra’ila”
“Dalilin wannan fitowar shine muyi kira ga gwamnatin Azarbeijan da ta daina takurawa ‘yan uwan mu musaman shugaban su Sheikh Haj Taleh Baqir Zadeh”, Inji wani Bala Hassan Bauchi daya daga cikin masu gangamin.
Bauchi ya kara da cewa, “Muna kuma kira ga al’ummar musulmi na duniya da su nuna goyon bayan su ga al’ummar Falasdinu da kuma Yemen”
Irin wannan gangamin na nuna goyon bayan ga al’ummar Falasdinu ya gudana a birnin kona ma.
Daruruwan musulmi ne suka tattaru a masallachin Fagge dake kano dauke da hotunan Baqir Zadeh yayin sauraron jawabi.
“Mun fito nan ne domin nuna goyon baya ga raunanan Azarbeijan wadanda ake tsare da su ba bisa ka’ida ba” Kamar yadda Dauda Nalado ya bayyana a muhallin gangamin.
Nalado ya cigaba da cewa, ” Ya kamata a saki Haj Taleh Zadeh domin ana tsare da su ne ba bisa ka’ida ba”
Mabiya Malam Zakzaky na harkar musulunc a Najeriya dai suna wannan gangami ne a dai dai lokacin da ake cika shekara 7 da waqi’ar Buhari ta Zariya.
Mabiyan na Malam Zakzaky sunngudanar da makamantan wannan taro a garuruwa mabambanta duk a mostin tunawa da waqi’ar ta buhari wacce ta gudana a shekara 2015, gami da kira ga gwamnatin Najeriya ta saki takardun malamin su daominn tafiya neman lafiya.