Shugaban majalisar musulman kasar Jamus ya bayyana irin munanan hare-haren da gwamnatin sahyoniyawa ta kai kan fararen hula a Gaza a matsayin laifin yaki.
A rahoton Anatoly, shugaban majalisar musulman ta tsakiya ta Jamus ya zargi Isra’ila da aikata laifukan yaki a yakin Gaza, ya kuma ce, munanan ayyukan soji da gwamnatin kasar ta aikata ya kai ga hukunta fararen hula Palasdinawa.
Ayman Mazik, shugaban majalisar koli ta musulmin kasar Jamus a wata hira da tashar ZDF ta gwamnatin kasar ya bayyana cewa: “Yanzu muna ganin irin azabar da ba za a iya misalta ba a Gaza. A mahangar mu, harin bama-bamai na yaki da Isra’ila ke yi laifi ne na yaki. Ya kuma jaddada cewa hukumcin gama-gari da ake yiwa farar hular Palasdinawa ba zai kai ga sasanta rikicin yankin gabas ta tsakiya ba.
Da yake bayyana halin da ake ciki na jin kai a Gaza da bakin ciki, Mazik ya yi kira da a kai dauki cikin gaggawa tare da tsagaita bude wuta a wannan yanki inda ya ce: “Dole ne a dakatar da amfani da makamai cikin gaggawa.” Ya kamata a taimaka wa mutane. Yakamata a samar da hanyoyi domin taimakon jin kai ya isa ga jama’a.
Kalaman na Mazik na zuwa ne bayan harin da jiragen yakin Isra’ila suka kai kan sansanin ‘yan gudun hijira na Jabalia da ke arewacin Gaza a ranar Talata, wanda ya yi sanadin mutuwar daruruwan mutane tare da jikkata.
Sojojin Isra’ila sun fadada kai hare-hare ta sama da ta kasa a zirin Gaza tun bayan harin ba-zata da Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba.
Tun kwanaki 26 da suka gabata sama da Falasdinawa 8,700 wadanda yawancinsu mata da kananan yara ne aka kashe sakamakon munanan hare-haren da Isra’ila ke kaiwa.
Source: IQNA HAUSA