Kananann yara ‘yan mata wadanda suka rafi kasar dubai domin samun rayuwa mafi inganci sakamakon talauci daya addabe su a gida Najeriya sun koka yayin da suka bayyana cewa ”Muna mutuwa cikin tsananin wahala gami da wulakanci”
‘Yan matan sun bayyana cewa babu abinda ya sanya su cikin wannan mawuyacin hali illah bakin talauci da gwamantin Najeriya ta jefa su a farkon lamari sa’annan kuma sun gamu da yaudarar daga agent da suke kaisu wanan kasa.
‘Yan matan sun bayyana cewa ‘Muna ayyukan kaskanci gami da hadari domin ciyar da kawunan mu kuma bamu da wata hanya sai wannan din”.
Wadannan ‘yan sunn bayyana cewa an yaudare su zuwa dubai amma hakan ya sabbaba musu shiga cikin wani mawuyacin hali wanda ya fi wanda suke ciki lokacin suna gida Najeriya tare da cewa lokacin suna gidan ma suna cikin mayuwacin hali na talauci gami da kaka su kayi.
”Yanzu muna yawo ne kwararo kwararo a bakuwar kasa babu gurin kwana” Inji daya daga cikin ‘yan matan amma ta alakanta hakan da tsananin talauci gami darashin aikin yi da gwamnatin Najeriya ta jefa ‘yan kasar ta ciki.
Tare da cewa hukumomi suna kokarin hanawa gami da jan hankalin mutane dangane da safarar mutane amma tsananin matsin rayuwa ya sanya mutane da dama sukan fada tarkon masu safarar mutanen.
‘Yan Najeriya wadanda ke cikin matsin rayuwa ko wadanda ke kokarin samun rayuwa mafi inganci sune suka fi fadawa cikin wannan yanayi a kasashen duniya.
Masana dai sun tabbatar da cewa ba’a taba samun matsin rayuwa a Najeriya irin wannan karon na mulkin Shugaba Muhammadu ba tare da cewa al’umma Najeriya sun kyatata masa zabo fuye da kowanne shugaban kasa da aka taba yi a tarihi.
Amma sai dai ana sa ran a fabrairun shekara mai zuwa za’a sake sabon zabe inda ake sa ran ‘yan Najeriyan zasu sake zabo sabon shugaban su, ko zasu dace wannan karon su zabo mmai gaskiya?
Ko zaben na ‘yan Najeriya yana da wata fa’ida wajen samun ingatacciyar rayuwar ‘yan kasa?
Ku bayyana mana ra’ayoyin ku a kasa.