Babban Shugaban Majalisar Ahlul-Baiti (AS) Ta Duniya A Ganawarsa Da Sheikh Zakzaky H: Kai Misali Ne Na Hakika Na “Mai Jahadi A Tafarkin Allah “Mujahid Faisabilullah”.
Ayatullah Ramezani: A kodayaushe muna shaukin ganawa da ku, kuma muna da girmamawa har zuciya gare ku. Kai ɗaya ne daga cikin fitattun mutane wajen kira ga ruhiyya da hankali. Abin alfahari ne a gare ku kasancewar ku kuna cikin manyan sojojin Limaman juyin juya halin Musulunci.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kamfanin dillancin labarai na Ahlul Baiti (AS) cewa, Ayatullah Reza Ramezani, babban sakataren majalisar Ahlulbaiti (AS) ta duniya ya gana da Hujjatul Islam wal Muslimeen Sheikh Ibrahim Zakzaky, babban shugaban Harka Islamiyyah A Nigeria a ranar Litinin Disamba 27, 2023.
A cikin wannan ganawa mai cike da shauki wanda kuma ta samu halartar Hujjatul Islam Wal-Muslimeen Mu’iniyan mataimakin shugaban majalisar duniya ta Ahlul-Bait (AS) da Hujjatul Islam Wal-Muslimeen Qadawi, mataimakin shugaban Fadada da gudanarwa da albarkatun wannan majalisa, Ayatullah Ramezani ya bayyana jin dadinsa a ganawar da suka yi da Shaikh Ibraheem Zakzaky, inda ya yi nuni da kwanakin da aka kai musu hare-haren matsorata da tsare su da aka yi ya kira su Sheikh din da cewa shi: (Mai Gyara Ne Da Aka Tsare Shi) wato da yaren farisi “Muslih Darband”.
Babban Sakatare Janar na Majalisar Ahlul Baiti (AS) ta duniya ya yi kira ganawarsa da Sheikh Zakzaky da iyalansa da cewa ganawa ce da ta sanya shi cikin farin, ya kuma kara da cewa: “A kodayaushe muna shaukin ganawa da ku, kuma muna da girmamawa har zuciya gare ku. Kai ɗaya ne daga cikin fitattun mutane wajen kira ga ruhiyya da hankali. Abin alfahari ne a gare ku kasancewar ku kuna cikin manyan sojojin Limaman juyin juya halin Musulunci.
A yayin da yake girmama irin kokari da kokarin da Mujahid Shaikh Zakzaky yake yi a Najeriya na yada koyarwar Shi’a, ya dauki shi a matsayin misali na hakika na Mujahid Faisabilullah tare da fatan cewa kokarin jihadi da tafarkin Shaikh Zakzaky su samu su ci gaba d dorewa.
Babban Shugaban Majalisar Ahlul-Baiti (AS) Ta Duniya ya ce: Manyan al’amura suna faruwa a duniya. Wannan juyi zai kai ga juyin juya halin Imam Mahdi (AS) kuma in sha Allahu adalcin Mahdawiyya ba mai nesa yake ba.
A wani bangare na wannan ganawar, Ayatullah Ramezani ya bayyana wasu daga cikin ayyukan majalisar duniya ta Ahlul Baiti (AS) inda ya ce: Akwai bangarori daban-daban a majalisar da suka hada da Wiki Shi’a encyclopedia cikin harsuna 22, kamfanin dillancin labarai na Ahlul Baiti (AS) – ABNA – a cikin harsuna 27. Tashar cibiyar sadarwa Ta Saqlain da kuma Ahl al-Bayt International University (A.S.) inda dalibai daga kasashe 29 na karatu.
Har ila yau Babban Sakataren Majalisar Ahlul-Baiti (A.S) Ramezani, ya yi ishara da bikin kaddamar da sabbin littattafan Majalisar Duniya Ta Ahlul Baiti (A.S) ya ce: “wanda an sanya a cikin kwanaki masu zuwa za a bayyana mujalladan littattafai dari da goma a cikin harsuna 22 da kuma littattafai biyar da aka karanta su a cikin Audiyon sauti.” Bayan ‘yan makonni kuma muna da bukin kaddamar da mujalladi 33 na littafai a cikin harsunan Farisa da Larabci game da Sayyidina Abu Talib (a.s.), wanda kawo yanzu babu wanda ya yi irin wannan aiki, kuma muna kokarin samun daya daga cikin manya-manyan Maraji’an Taqlid domin ya samu halartar wannan biki.
Ya ce: A halin yanzu malamai masu Tabligi na cikin gida suna yin hadin gwiwa da Majalisar Duniya ta Ahlul-Baiti (AS), wanda daga cikin wadannan wadannan masu Tabligin sun fito ne daga nahiyar Afirka, kuma wannan wata babbar dama ce.
Abubuwa da dama sun faru a sassa daban-daban na Majalisar Ahlul-baiti (AS) ta duniya kuma wannan majalisi ta yi matukar tasiri.
Mun kuma shaida yadda aka fara gudanar da taruka na gida a kasashe daban-daban na duniya.
Har ila yau Babban Sakataren Majalisar Ahlul-Baiti (AS) ya karrama irin sadaukarwar da matar Mujahid Sheikh Ibrahim Zakzaky ta yi, tare da addu’ar Allah Madaukakin Sarki da Ya ba wa wannan baiwar Allah lafiya.
Hujjatul Islam wal Muslimin Sheikh Ibrahim Zakzaky, yayin da yake nuna jin dadinsa da ganawar da Ayatullah Ramezani ya yi, ya yi ishara da manufar Majalisar Ahlul Baiti (AS) ta duniya inda ya bayyana cewa: Wannan majalissar tana tallafa wa ‘Yan Shi’a ta bangarori daban-daban tare da kuma mara musu baya, musamman a fagen yada mazhabar Ahlul Baiti.A).
Ba mu san Mazhabar Ahlul-baiti ba kafin nasarar juyin juya halin Musulunci. A lokacin ana ganin ‘yan Shi’a a matsayin masu karkatattun tunani.
A lokacin ina dalibi a 1973, wani farfesa yana magana a cikin ajin akidar Shi’a yana da’awar cewa abubuwan da musulmi suka dauka haramun ne, ‘yan Shi’a suna daukarsu halal, kaga me musulmin da ya ji irin wadannan abubuwa zai yi tunani dangane da ‘yan Shi’a?
Ya ci gaba da cewa: Bayan nasarar juyin juya halin Musulunci na Iran, wannan juyin juya halin Musulunci ya yi tasiri matuka a kan musulmi a Nijeriya, kuma a kasar nan ne aka haifi yunkurin Istbasar, amma makiya a Nijeriya sun fara yada farfagandar kyamar Shi’a da kuma suka yi mana zargin cin mutunci ga wasu Sahabbai da wasu daga cikin matan Manzon Allah (SAW), musamman abun yayi tsanani bayan waki’ar Zariya.
Jagoran Harkar Musulunci a Najeriya ya kara da cewa: A waki’ar Zariya an yi yunkurin kawai da mu ‘yan Shi’a a Najeriya gaba daya, amma kaddarar Allah ta kasance akan zamu wanzu, kuma kira ga Musulunci yana karuwa da yaduwa.
Sun sa harkar Musulunci ta Najeriya takara karfi sama da wanda ta ke da shi a da. Yanzu mun fi kowane lokaci ƙarfi saboda juriyarmu da yawanmu.
Yawan ‘yan Shi’a a Najeriya ya karu kuma babu wani abu da ya tsaya a cikin ayyukanmu a wadannan shekarun, sai dai ma sun samu ci gaba.
A kwanakin nan, mun gudanar da bikin cika shekaru takwas da aukuwar waki’ar Zariya, wanda ya zo daidai da zagayowar ranar shahadar Sayyida Zahra (AS), inda jama’a da dama suka fito kan tituna a garuruwa daban-daban na Nijeriya.
Yayin da yake ishara da kubutar da shi daga waki’ar Zariya, Shaikh Mujahid Zakzaky ya ce: A wannan waki’a, sojoji sun harbe ni da matata kai tsaye.
A cikin wannan waki’a na ga abubuwan al’ajabi da yawa kuma duk da an kona min gidana tare da jefa harsashin yaki da aka yi min, Amma Allah Ta’ala ya qaddara min tsira.
Da idona na gani kashina ya tsage harsashin ya shiga cikin idona, amma ban ji wani zafi ba. Har yanzu ina da harsashi daga wannan waki’a, musamman a kaina. Yarana 6 daga cikin ‘ya’yana sun yi shahada a cikin shekarun da suka gabata kuma daya ne kawai daga cikin ‘ya’yana maza da mata biyu suka rage.
Babban Shugaban Harkar Musulunci a Najeriya ya bayyana jin dadinsa da kokarin da majalissar Ahlul-baiti ta duniya (AS) ke yi na kare ‘yan Shi’ar Najeriya, ya ce: Ina godiya ga wannan majalisa da ta kasance tare da mu tun farkon waki’ar Zariya. Yanayin bayyanar Imam yana a shirye kuma ku kuna share fagen da shirye-shirye wajen bayyanarsa. Duk abin da na yi nasara ce da dacewa ta Allah, kuma ban yi wani aiki ba da har ya zamo na zama wata alama ta yaduwar Shi’anci ba.
A karshen wannan ganawar, babban sakataren Majalisar Ahlul-baiti (AS) ya mika wa Sheikh Ibrahim Zakzaky tuta da aka kawata da sunan Imamuz Zaman (AS) tare da yaba kokarin wannan babban malamin Shi’a.
Mujahid Mujahid
Source: ABNAHAUSA