Jose Mourinho ya sha kayi mafi muni a tarihin aikinsa na horas wa, bayan da Roma ta sha kashi a hannun Bodo/Glimt da ci 6-1 a gasar Europa League.
Ana wasa ci 2-1 kafin atafi hutun rabin lokaci, amma kawai sai lamari ya sauya tare da bada mamaki bayan dawowa daga hutu, duk da sauye-sauyen ‘yan wasa har sau 5 da Mourinho yayi, amma sai da akayi musu dukar kawo wuka har 6-1.
Wannan ne karon farko da wata kungiya da Mourinho ke jagoranta ta sha ruwan kwallaye har 6 ko sama da haka a wasa guda, a wasanni 1,0008 na rayuwarsa ta koci.
Kafin wannan lokaci rashin nasarar mafi muni shine lokacin da Barcelona ta yi musu kacha-kacha da ci 5-0 a shekarar 2010 lokacin yana jagorantar Real Madrid.
A wani labarin na daban yau ake dawowa wasannin gasar Kwallon kafa ta Europa, domin karasa wasannin matakin da ya kunshi kungiyoyi 16, bayan hutun dole da annobar korona ta sa aka dakatar da gasar.
Cikin kungiyoyin da zasu fafatawa wasannin na yau da gobe, harda Manchester United da Wolves da Rangers da Inter Milan da kuma Roma.
Bari mu duba jadawalin kungiyoyin da zasu hadu a wasannin.
Da misalin 5 : 55 pm: FC Copen-hagen v Istanbul Basaksehir (1 – 0 a wasan zageye na farko)
Yayin da Shakhtar Donetsk v Wolfsburg ( 2-1 wasan farko) .
Sai kuma da misalin karfe 8pm agogon: Inter Milan v Getafe (kuma tun farko basu yi wasa zaye na farko ba)
Yayin da Manchester United v Lask ( 5-0 zageyen farko ) .
Sai kuma wasannin da za’a fafata gobe Alhamis, 6 ga wata idan Allah ya so.
Bayer Leverkusen v Rangers zasu fafata da misalin karfe 5:55pm( 3-1 wasan farko)
Yayin da Sevilla v Roma.(an dage wasansu na farko)
Basel v Eintracht Frankfurt da karfe 8pm ( 3-0 wasan farko)
Sai kuma WOLVES v Olympiakos (wanda sukayi canjarasa 1-1 farkon).
*wasa tsakanin Inter Milan v Getafe da kuma Sevilla v Roma, shine wasan sun a farko a zageyen na 16, saboda dage wasannin na farko da akayi saboda koronavirus.