Dan wasan tsakiya na Tottenham, Dele Alli yace tsohon kocinsa Jose Mourinho ya cika mayar da hankali a kan abokan hamayya a yayin shirye shiryen tinkarar wasa.
Sai dai yanzu dan wasan ya zama mai murza leda a kullayaumin a karkashin mai horarwa, However, Nuno Espirito Santo.
Dan shekara 25 din kasance cikin ‘yan wasan tsakiya da ake damawa da su a tsakiyar filin Tottenham a wannan zamani na Koch Nuno, kuma ya buga ilahirin wasannin gasar Firimiyar Ingila na wannan kaka tun da aka fara.
Alli ya shaida wa manema labarai cewa Mourinho yana da dabi’ar daukar lokaci yana nazari a kan abokan hamayya, maimakon ya mayar da hankali a kan abin da ya dace a yi.
A wani labarin mai kama da wannan kungiyar kwallon kafa ta Tottenham ta sanar da nadin Nuno Espirito Santo a matsayin mai horar da tawagarta kan kwantiragin shekaru 2 da nufin maye gurbin Maurinho da ta kora a watan Aprilu.
Bayan tafiyar Mourinho Tottenham ta yi amfani da Ryan Mason mai shekaru 29 da ya jagoranci tawagar zuwa karshen kakar da ta gabata.
Da ya ke sanar da matakin a shafinsa, Nuno ya bayyana horar da tawagar Tottenham a matsayin abin alfahari gare shi.
Kafin yanzu dai Tottenham ta yi zawarcin tsohon kocin AS Roma Paulo Fonseca bayan gaza cimma jituwa da Nuno a farko.
Haka zalika kungiyar wadda ta rasa sukunin taka leda a gasar cin kofin zakarun Turai na kaka mai zuwa, ta yi kokarin dawo da tsohon manajanta Mauricio Pochettino da ke jagorancin PSG a yanzu.