Moroko Ta Kai Hari Da Jirgin Sama Maras Matuki A Yankin Yammacin Sahara.
Jaridar “Ra’ayul-Yau” ta ambato wata majiya a kasar Murtaniya tana cewa; Jirgin yaki maras matuki na kasar moroko ya kai hari akan wani yanki dake iyakar Murtaniya da yammacin Sahara.
Majiyar ta ci gaba da cewa; Jirgin ya kai hari ne akan ayarin wasu manyan motocin daukar kaya wanda kuma ya haifar da asara ta dukiya.
Harin na jiya Lahadi an kai shi ne a lokacin da motocin suke tsaye, matukansu kuma suna salla, sai dai babu wani rahoto da ya amabata cewa an sami wanda ya jikkata. Sai dai daya daga cikin manyan motocin ta kone kurmus.
Wannan dai shi ne karo na biyu da jirgin yaki maras matuki na kasar Moroko ya kai hari a yankin na yammacin Sahara a cikin watanni biyar.
READ MORE : Libiya; Dakarun Haftar, Sun Janye Daga Kwamitin Yarjejeniyar Berlin.
A can yankin yammacin Sahara an bayyana cewa; manufar harin dai shi ne datse isar da kayan masarufi zuwa ga daya daga cikin sansanoni ‘yan gudun hijirar yankin.
READ MORE : Tarayyar Turai EU Ta Sanar Da Dakatar Horar Da Sojojin Kasar Mali.
READ MORE : Nasrullah; Abin Da Ke Faruwa A Falastinu Manuniya Ce Kan Makomar Isra’ila.