Morocco;’Yan Jarida Sun Bayyana Yarjejeniyar Kafofin Yada Labarai Da Isra’ila A Matsayin Tsokana.
Wani gungun ‘yan jaridu a Morocco, ya bayyana kulla yarjejeniyar kafofin yada labarai da Isra’ila a matsayin tsokanar ‘yan kasar da al’ummar falasdinu da al’umma gabadaya.
Wannan dai na zuwa ne ‘yan kwanaki bayan bude wani ofishin yada labarai na wata tashar Isra’ila a kasra ta Morocco.
Sanarwar da gomman ‘yan jaridu suka sanya wa hannu, ta yi allawai da bude ofishin tashar talabijn ta Isra’ila “i24news” a kasar ta Morocco da kuma bikn bude tashar da akayi a yankin Chilla mai tarihi dake birnin Ramat.
Gungun ‘yan jaridan sun bukaci hukumomin Morocco dasu gaggauta rufe tashar ta ‘yan mamaya na Isra’ila.
READ MORE : Iran Ta Yi Watsi Da Rahoton Guterres Kan Take Hakkin Bil’adama A Kasar.
Dama dai bangarori da dama a Morocco sun kalubanci alakar da kasar ke kullawa da mahukuntan yahudawa ‘yan mamaya na Isra’ila musamman a baya bayan nan.
READ MORE : Amurka Ta Kai Makamai Da Kayakin Yaki Daga Siriya Zuwa Iraqi.
READ MORE : Richado Sa Pinto Ya Zama Sabon Kocin Kungiyar Kwallon Kafa Ta Esteghlal Ta Iran.
READ MORE : Hajji; Alamar hadin kai da hadin kai.
READ MORE : Nakiya ta kashe wani sojin Majalisar Dinkin Duniya a Mali.