Morocco Ta Kirayi Jakadanta A Tunisiya Saboda Karbar Bakuncin Shugaban Polisario A Kasar.
Morocco ta kirayi jakadanta a Tunisiya, bayan da shugaban kasar Tunisiya Kais Saied ya karbi bakoncin shugaban kungiyar Polisario Ibrahim Ghali a Tunisiya domin halartar babban taron ci gaban Afirca na Tokyo “TICAD 8”.
A cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Morocco ta fitar, ta ce, Tunisiya ta dauki wasu matakai wadada suke jawo rashin jituwa a tsakaninta da masarautar Morocco, wanda kuma hakan ya tabbata a fili a wanann karo, duk kuwa da cewa daga cikin tsarin taron “TICAD” wanda ya hada mahangar Japan da Afirca hard a yaki da ta’addanci, wanda kuma Tunisia ya amince da hakan a cikin ka’idojin taron.
Ma’aikatar harkokin wajen Morocco ta yi nuni da cewa, Tunisiya ta yanke shawarar gayyato ‘yan tawayen Polisario, kuma liyafar da shugaban kasar Tunusiya Kais Saied ya yi wa shugaban kungiyar Ibrahim Ghali, wani lamari ne mai hatsarin da ba a taba ganin irinsa ba, wanda ke tabbas ya bakanta ran al’ummar Moroko da dakarunsu, a cewar bayanin..
Dangane da wannan matsaya ta kiyayya da ke cutar da alakar ‘yan uwantaka da alaka tsakanin kasashen biyu, Masarautar Morocco ta yanke shawarar kin halartar taron koli na TICAD karo na 8, wanda za a yi a Tunisia a ranakun 27 da 28 ga watan Agusta, tare da kuma kiran jakadan Morocco da ke Tunisiya domin tattaunawa.
Shugaban kasar Tunisiya Kais Saied ya karbi bakuncin sakataren kungiyar Polisario Ibrahim Ghali da wata tawaga da ke yi masa rakiya domin halartar taron na TICAD 8.