MJTF Ta Kashe ‘Yan Ta’adda Fiye Da Dari Takwas A Tafkin Chadi.
Rundunar Sojin hadin gwuiwa dake yaki da Yan ta’adda a Yankin Tafkin Chadi ta sanar da kashe mayakan Boko Haram sama da 800 a cikin watanni biyu da suka gabata a tsibirin dake tsakanin kasashen Najeriya da Nijar da Kamaru da kuma Chadi.
Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ruwaito wani rahotan rundunar na cewar tsakanin ranar 28 ga watan Maris zuwa 4 ga watan Yuni, hadin gwuiwan sojojin sun gudanar da samamen hadin kai a Tsibirin dake Tafkin Chadin da kuma kauyukan sa inda suka kashe tarin mayakan boko haram da na ISWAP.
Rahotan ya bayyana samun gagarumar nasara a cikin samamen da suka yi wanda ya kai ga hallaka mutane 805 da kama ko lalata motocin su 44 da babura 22 da kuma tarin kanana da manyan makamai.
Sanarwar tace akalla sojoji 3,000 suka shiga aikin samamen ta kasa da ruwa da kuma sama wanda ya kunshi sojojin kasashen 4 na Najeriya da Nijar da Kamaru da kuma Chadi inda suka kwashe kwanaki 45 suna yi.
Rahotan yace sojojin sun kwace tarin makamai da bama bama bayan gano inda ake sarrafa su, yayin da wasu sojojin Nijar kusan 20 suka samu raunuka sakamakon tashin abin fashewar.