Ministan yada labaran kasar Yemen Daifullah Al-Shami, ya bayyana a taron da aka gudanar ta gidan yanar gizo da aka watsa a wurin taron girmama shahidan ‘yan jaridan Gaza, cewa: ‘yan jarida ne za su dawwamar da tarihi kuma su rubuta shi da kalmomin haske.
Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na kasa da kasa na Ahlul Bayt (AS) – ABNA – ya habarta maku cewa: a wajen taron tunawa da shahidan ‘yan jaridan Gaza da aka gudanar a zauren majalissar Ahlul-baiti (a.s) ministan yada labaran kasar Yemen Daifullah Al- Shami” ya ce yayin da yake gudanar da jawabi ta hanyar kafar watsa shirye-shiryen gidan yanar gizon: ma’abota alkaluma madaukaki masu dauke kyamara da mutane masu aiki a kafafen yada labarai sun sami damar nuna ayyukan makiya masu laifi ga duniya.
Bayanin Ministan Yada Labarai na kasar Yaman shi ne kamar haka.
بسم الله الرحمن الرحیم
الحمد لله رب العالمین والصلاة والسلام علی سیدنا محمد(ص) وعلی آله الطیبین الطاهرین
Yan uwa masu daukaka ina mai mika maku gaisuwata:
Abin farin cikinmu ne kasancewarmu tare da ku a wannan taro domin girmama shahidan tafarkin gaskiya wadanda suka yi shahada a tafarkin mutunci da aikin yada labarai, da kuma nuna hakikanin gaskiyar laifukan da yahudawan sahyoniya da makiya Amurka suka aikata a kan ’yan’uwanmu a Palastinu.
A yau, muna girmama wadannan shahidai tare da yaba wa irin rawar da dukkan maza da mata suka taka a fagen yada labarai na ‘yan jarida.
Sun bayar da mafi kyawun dukiyoyinsu, wato rayuwarsu, ta hanyar isar da wannan siffa ta gaskiya, ta yadda za a isar da sako mai kyau ga wannan al’umma wanda al’ummar Palastinu da sauran dukkan ‘yantattun al’umma ba za su taba yin kasa a gwiwa ba kan wannan lamari.
Suna aiki ne ta hanyar bayyana laifuffukan abokan gaba na Amurka da sahyoniyawan da kuma wannan komar yahudawan sahyoniyawan da ke neman kawar da gaskiya, rufe baki, canza ma’auni, mai da makashi a matsayin shahidi da shahidi maimakon mai aiwatar da kisa.
A yau a wannan taro mun yaba da matsayin dattijan Palasdinawa da jarumai da jajirtattu a dukkanin fagage da ma dukkanin sojojin da ke gwagwarmaya a dukkanin kasashen da suka hada da Yemen, Falasdinu, Labanon, Iraki, Siriya, Tehran da dukkanin bangarorin fagagen gwagwarmaya.
Muna rokon daukacin ma’abuta kafafen yada labarai da masu alkalamai yantattu da ma’abota runduna da su cika aikinsu; Domin kafofin watsa labarai kayan aiki ne mai ƙarfi da inganci kuma suna da nauyi mai tasiri.
Idan ba ku cikin wannan yaƙin, to yaushe kuke son kasancewa a acikinsa?.
Haɗin kai na murya wajen goyon bayan Mujahidai da Palastinu da Gaza da kuma dukkan yankunan duniya ana ɗaukarsa a matsayin jihadi kuma tsakiyar ƙa’idar da ta yi Allah wadai da zalunci da aikata laifuka da kisan kiyashi.
A yau, muna shaida irin laifukan da ba a taɓa gani ba a cikin komar yahudawa-Amurka da Isra’ila, wanda ke neman kawar da gaskiya da kuma canza ma’auni, kuma muna shaida yadda ma’abuta alƙaluma masu daraja da kyamara da kuma mutane masu aiki a cikin wannan filin suna nuna halin gaskiyar munin wannan makiya masu mugunta da ayyukansu ga duniya.
Daga nan muna girmama wannan kokari nasu, muna shaida musu cewa kun wuce babban mataki, kuma ba za a taba tattake jinin shahidai da ‘yan jarida a banza ba.
Maganarsu da muryoyinsu da manufofinsu sun samo asali ne daga gaskiya kuma su ne masu rike da tuta ta gaskiya da fallasa mungan laifuka. Muna mika godiyarmu ga wadannan shahidan tare da jajantawa iyalansu.
Har ila yau, muna sanar da sauran ‘yan jarida da ‘yan jarida masu ‘yanci a fadin duniya cewa, kada azzaluman masu laifi su tsorata ku, domin ku ne jakadun magana da ingantaccen jawabi, kuma ku ne za ku dawwamar da tarihi ku rubuta shi da kalaman haske.
Za ku shaida wa duniya cewa an samu wata al’umma da mutane da suka tsaya tsayin daka wajen adawa da girman kan duniya kuma akwai mutane mazaje da ke dauke da kyamara a kafadarsu da suka rubuta da alqalaminsu da bayar da jininsu a matsayin kyauta a fagen ‘yanci da kuma daukaka kafofin watsa labarai masu daraja su ka kasance tsarkakku daga kowace irin kazanta.
Haka nan kuma ya suna masu shaida wa duniya cewa, an murtsuke makaman Amurka da sahyoniyawan a karkashin kafafun Mujahidan Gaza, Palastinu da dukkan kasashen gwagwarmaya da Jihad.
Muna rokon Allah ya jikan wadannan shahidan, ya kuma baiwa wadanda suka tsira da rayukansu hakuri da juriya.
Ina fatan wannan ƙoƙarin aiki da aka shirya a cikin yanayin karramawa zai zama wani aiki da zai gabatar da wadannan shahidai a matsayin wata alama ta girmamawa ga dukkanin kafafen yada labarai na duniya.
Assalamu alaikum da rahama da albarkar Allah Ta’ala
Ya kamata a lura da cewa, an gudanar da taron tunawa da shahidai na Gaza a yau ranar Litinin 15 ga Disamba 2024 a nan Tehran, bisa daukar nauyin Majalisar Ahlul-Baiti (AS) da Kamfanin Dillancin Labarai na Abna.
Ya kamata a lura da cewa, an gudanar da wannan taro ne da jawabai kai tsaye da kuma bidiyo daga nesa daga Ayatullah Riza Ramezani, babban sakataren majalisar Ahlul-Baiti (AS) ta duniya da kuma wasu manyan mutane daga kasashen Palastinu, Yaman, Iraki, Turkiyya da Indonesia, tare da gabatar da jawabai tare da halartar manajojin kafofin watsa labarai na duniya da masu fafutuka.
Source: ABNAHAUSA