Ministan ya ce wannan kwafin kur’ani yana da matukar muhimmanci ga dukkanin al’ummar kasar Serbia, amma kasantuwar Azhar na babbar cibiyar ilimi ta musulunci,a madadin al’ummar serbia ya bayar da kyautar wannan kwafin kur’ani ag wannan cibiya.
Kasar Serbia dai tana da kyakkayawar alaka da kasar Masar, musamman ma tun bayan yakin Bosnia da aka yi, inda daga bisani aka yi sulhu kuma sabiyawan suka nuna nadama kan abin da wasu daga cikinsu aikata kan musulmi.
A halin yanzu dai cibiyar azhar ta karbi wannan kwafin kur’ani, tare da sanya shi a cikin jerin littafaii na tarihi da take adanawa.
A wani labarin na daban jaridar Yaum Sabi ta bayar da rahoton cewa, musulmi da kiristoci suna yin aiki tare wajen sake gina wani tson masallaci da aka gina shi daruruwan shekaru da suka gabata a lardin Alminya a kasar Masar.
Daya daga cikin masu jagorantar aikin sake gina wannan masallaci ya bayyana cewa, wannan masallaci yana daga cikin tsoffin wurare na tarihi da yankin, amma an wayi gari masallacin an kaurace masa saboda rashin kula da lalacewar gininsa.
Wani mutum daga cikin dattijan garin mai Imad Shuhat wanda kirista ne, shi ne ya bayar da shawara kan cewa ya kamata a sake gyara masallacin, kasantuwar cewa yana daga cikin muhimman wurare na tarihi na musulmi da suke yankin.
Wannan shawara ta samua wurin musulmi da kuma mabiya addinin kirista, a kan haka suka hadu baki daya suna gudanar da aikin sake gina wannan tsohon masallaci.