Ministan Tsaron Taliban; Amurka na kai wa Afghanistan hari daga sararin samaniyar Pakistan.
Mukaddashin ministan tsaro na gwamnatin rikon kwarya ta Taliban ya bayyana cewa Pakistan na baiwa jiragen Amurka marasa matuka a sararin samaniyarta domin kai hari a Afganistan.
Mullah Yaqub Mujahid, mukaddashin ministan tsaro na kungiyar Taliban, ya bayyanawa tare da babban hafsan hafsoshin kungiyar a wani taron manema labarai a birnin Kabul cewa jiragen Amurka marasa matuka na shiga Afghanistan daga Pakistan.
A cewar Mullah Yaqub jiragen da ba a san ko su waye ba da ke sintiri a sararin samaniyar kasar ta Afganistan na Amurka ne.
Ya dauki wannan mataki na Amurka a matsayin cin zarafi ga kasar Afghanistan.
A cikin ‘yan kwanakin nan dai an ga sintiri da jiragen yaki marasa matuka a wasu larduna.
Mukaddashin ministan tsaron Taliban ya yi nuni da cewa, sun bayyana damuwarsu kan hakan a tattaunawar da suka yi da bangaren Amurka.
Idan dai ba a manta ba, an kashe Ayman al-Zawahiri, shugaban kungiyar al-Qaeda, sakamakon harin da jiragen yakin Amurka marasa matuka suka kai a yankin koren tsaro na birnin Kabul.
Har yanzu dai kungiyar ta Taliban ba ta tabbatar da wannan ikirari ba kuma ta ce tana gudanar da bincike kan lamarin.
Mulla Yaqoub ya bayyana a taron cewa kisan al-Zawahiri zargi ne kawai kuma ana ci gaba da gudanar da bincike kuma za a bayyana sakamakon.