Ministan tsaron kasar Kamaru Joseph Beti Asomo Jeshep ya ja hankalin takaransa ministan cikin gida Paul Atanga Nji kan yawaitan shingayen binciken ababen hawa da ake samu daga birnin Doula har zuwa Douala zuwa Maroua dake arewacin ciki harda na bogi.
Wannan al’amari dai na kasancewa ga matafiya jerangiyar bata lokaci mai wahalar gaske, kamar yadda ministocin 2 suka sanar a cikin wata sanarwar da suka fitar a ranar 5 ga wannan wata na Afrilu.
Ministan tsaro Joseph Beti Assomo ya ce waddannan shingayen bincike da basa kan ka’ida mahukunta ne suka kafa su. Inda ya bukaci takwaransa na cikin gida Paul Atanga Nji da ya sanar da abukan aikinsa kantomomin kananan hukumomi da na manyan yankuna da gwamnoni da su rage yawan su tare da samar da na gamin gambizar jami’an tsaron.
Sai dai ana ganin mawuyacin abu ne kiran ya samu karbuwa ganin ba a karon farko ke nan ba mahukunta ke kokuwa kan yawaitar shingayen jami’an tsaron kan hanyoyin motar kasar, al’amarin dake haifar da jerangiya ga matafiya ba tare da kwalliya ns biyan kudin sabulu ba.
A wani labarin na daban Kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch ta zargi gwamnatin Kamaru da na Amurka da aikata “take hakkin dan adam” mafi muni kan ‘yan kasar da dama da Amurka ta mayar da su kasar da ke yankin tsakiyar Afirka.
Inda suka fuskanci tsarewa ba bisa ka’ida ba; bacewar wasu; azabtarwa da fyade, da kuma sauran tashin hankali, ko kuma karban cin hanci.
Yankin ‘Yan aware
Kusan dukkanin wadanda Amurkan ta dawo da su gida Kamaru, sun fito ne daga yankin tsirarun masu amfani da turancin Ingilishi a yammacin kasar, inda mayakan ‘yan awaren dake neman ballewa domin kafa kasar Ambazonia ke fafatawa da sojojin gwamnati da suka shafe shekaru biyar cikin kazamin rikici, inda Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyi masu zaman kansu ke zargin bangarorin biyu da cin zarafin jama’a.
Rahotan yace “da yawa daga cikin mutanen sun fuskanci cin zarafi da suka hada da amfani da karfi fiye da kima, rashin kulawar likita, da sauran cin zarafi a hannun hukumomin Shige da Fice da Hukumar Kwastam na Amurka.
Amurka ta keta ‘yancin mafaka
Kungiyar tace da wannan mataki da Amurka ta dauko na maido da ‘yan kasar Kamaru gida duk da ta kwana da sanin barazanar zalunci da suke fuskantar da azabtarwa, to lallai ta keta ‘yan mafaka da na kare hakkin bil’adama.”
Gwmanatin Trump
Rahoton ya ce an kori mutanen ne a karkashin gwamnatin tsohon shugaban Amurka Donald Trump, “wanda ke da tsattsauran ra’ayi na shige da fice, da takaita samun mafaka, da kalaman wariyar launin fata,”
Gwamantin Biden
HRW tace, yayin da gwamnatin shugaban Amurka Joe Biden ta “dauki kyakkyawar matakin soke wani jirgin ‘yan kasar Kamaru zuwa gida a watan Fabrairun shekarar 2021, amma abin takaici ta kori ‘yan kasar da dama cikin watan Oktoba.