Ministan harkokin wajen kasar Siriya Faisal Moqdad, yayin da yake ishara da fifikon yin kwaskwarima ga alakar kasashen Larabawa, ya ce, “A hankali yawancin kasashen Larabawa suna fahimtar komawar kasar Siriya cikin kungiyar hadin kan kasashen Larabawa da hadin gwiwar kasashen Larabawa.”
Kamfanin dillancin labaran Ahlul Bait As ABNA ya kawo maku Rahoto alakar d ake gudana da kasar siriya da sauran kasashen larabawa kamar yadda rahoton na Al Arabi Al-Jadeed, Faisal Moqdad ya kara da cewa: Syria ba ta gaggawar komawa kungiyar kasashen Larabawa, kuma gyara huldar dake tsakanin kasashen biyu abu ne mai muhimmanci.
Ya ce: “Idan har ya zamo sadaukarwa ne idan kasar Siriya ta fice daga cikin kasashen Larabawa na wani dan lokaci kadan, idan kuma ya zamo Larabawa zasu samu sauki daga wasu matsaloli, to babu laifi a cikin hakan.
” Syria ba za ta taba zama alhakin rarrabuwar kawuna da sabani tsakanin kasashen Larabawa ba.