Ministan harkokin waje qatar sheikh muhammad bin abdurrahman Althani yana ziyarar aiki a kasar jamhuriyar musulunci ta Iran a kokarin sa na kyautata alaka tsakanin kasar da sabuwar gwamnatin jamhuriyar musulunci ta Iran karkashin jagoran shugaba Sayyid Ibrahim Ra’esi.
Kamar yadda kafar sadarwa ta Aljazeera ta tabbatar ya nuna cewa ministan harkokin wajen na kasar qatar yana ziyarar ne a jamhuriyar musulunci ta ta Iran jim kadan bayan ya gana da ministan harkokin wajen amurka anthony blinken.
A yayin ganawar sa da takwaran sa da jamhuriyar musulunci ta Iran, minstan harkokin wajen na qatar ya nuna bukatar kasar sa na kyautata alakokin siyasa, diflomasiyya gami da tattalin arziki da jamhuriyar musulunci ta Iran.
A wani mataki na tabbatar da kyakykyawar alaka da sabuwar zababbiyar gwamnatin jamhuriyar musulunci ta Iran din ya taya shugaba Ayatullah Sayyid Ibrahim Ra’esi bisa lashe zaben da yayi, sa’annan ya taba takwaran sa na jamhuriyar musulunci ta Iran din Agaye Abdullahiyan murna sa’annan yayi fatan za’a sami cigaba gami da kyakykyawar alaka tsakanin kasashen biyu.
A wani labarin na daban kungiyar taliban tayi da’awar cewa ta karbi iko da yankin panjshar na kasar afghanistan, labarin bangaren ‘yan aware suka musa inda suka bayyana cewa har yanzu yanzkin na panjshar bai fada hannun sabuwar gwamnatin karkashin jagorancin kungiyar taliban din ba.
Sabuwar gwamnatin ta taliban dai tuni ta bayyana kafa sabuwar gwamnati, inda ta nada mukaman gwamnati kama daga kan firayi ministan, minstan harkokin kasashen waje da dai sauran su.
Masana siyasar duniya dai suna kallon wannan taliban din da yau a matsayin sabuwar taliban wacce bata da ra’ayin wahabiyanci amma da dama suna taradduidn sahihancin sake tunanin mambobin kungiyar ta taliban inda suke tsoron kada daga baya a samu canjin lamurran a kasar ta afghanistan.
Kasar amurka dai tuni da nuna damuwar ta bisa shan kayen da tayi a kasar ta afghanistan inda bayan shafe shekaru ashirin a kasar ta afghanistan ta fice ba tare da ta cimma muradan ta ba.