Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Tattauna Da Takwaransa Na Ukraine.
Ministan harkokin wajen kasar Iran, Hossein Amir Abdolahian, ya tattauna ta wayar tarho da takwaransa na Ukraine Dmytro Kuleba.
Bangarorin biyu sun tattauna kan batutuwan da suka shafi kasa da kasa musamman rikicin Ukraine.
Sun kuma tattauna batun kare ofisoshin diflomatsiyya da aikewa da tallafin jin kai dama batutuwan da suka shafe alakar dake tsakaninsu.
READ MORE : An Shiga Kwana Na Ashirin Na Rikicin Rasha Da Ukraine.
Iran ta bakin ministan harkokin wajenta ta ce tana goyan bayan duk wani yunkuri na shawo kan rikice rikice a duniya, musamman a Ukraine, Afganistan, Yamen da ma wasu kasashe ba tare da siyasa mai harshen damo ba, a cewar Amir Abdollahian.
A wani labarin kuma ministan harkokin wajen kasar ta Iran, zai isa birnin Moscow na kasar Rasha a wannan Talata, domin tattauna batutuwan da suka shafi yankin dama yarjejeniyar nukiliyar Iran.