Wata majiyar sojan ruwan kasar Mexico ta bayyana a cewa, an kama wani da ake zargi da laifin safarar miyagun kwayoyi a cikin jerin mutane 10 da hukumar FBI ta ke nema ruwa a jallo.
Ya sha dauri a baya
Sai dai an kama shi a wancan lokacin, tare da yanke masa hukuncin daurin shekaru 40 a gidan yari saboda kisan Camarena, yayin da a shekarar 2013, wata kotu a Mexico ta ba da umarnin a saki Caro Quintero bayan ya kwashe shekaru 28 a kurkuku.
Sai kuma Kotun kolin Mexico ta soke hukuncin, amma Caro Quintero ya tsere a lokacin.
Dangantakar Mexico da Amurka
Lamarin ya jefa dangantakar Amurka da Mexico cikin rikici, kuma an dauki shekaru da dama kafin hukumomin yaki da fataucin miyagun kwayoyi a bangarorin biyu na kan iyaka su sake maido da dangantaka.
Caro Quintero, wanda ake yi wa lakabi da “Rafa,” Hukumar FBI ta sanya tukaicin dala miliyan 20 ga duk wanda ya gano inda ya yake, bayan bayyana shi a matsayin “mai matukar hadari.”
Source:RFI