Sabon dan wasan da PSG ta saya daga Barcelona Lionel Messi ya yi nasarar zura kwallonsa na farko yayin haduwarsu da Manchester City a daren jiya talata, kwallon da ke matsayin ta 74 da tauraron na Argentina ya zura a karkashin gasar ta cin kofin zakarun Turai
Wasan na jiya dai shi ne na biyar da Messi ya dokawa sabuwar kungiyar tasa kuma minti na 264 a fili ba tare da kwallo ba gabanin nasarar kan Manchester City kungiyar da ke karkashin tsohon manajan Messin wato Pep Guardiola kocin da suka kafa gagarumin tarihi tare da dan wasan yayin taka leda a Barcelona.
A zantawarsa da manema labarai bayan kammala wasan, Messi ya tabbatar da cewa ya matukar kaguwa yaga kwallonsa ta farko a PSG bayan taka leda a jerin wasanni ba tare da kwallo ba.
A wani labarin na daban mujallar Fobes ta rawaito cewa, Cristiano Ronaldo na Manchester United ya yi wa Lionel Messi na PSG fintikau, inda a yanzu ya dare duk wani dan wasan kwallon kafa a duniya wajen samun albashi mafi tsoka.
Dan wasan zai samu Dala miliyan 70 daga albashinsa da kuma kudaden alawus-alawus da Manchester United za ta ba shi.
Sauran kudaden za su fito ne daga kamfanonin da dan wasan ke yi musu tallace-tallace kamar Nike da Herbalife da sauransu.
Mujallar ta Forbes ta ce, Ronaldo na cikin sharaharrun ‘yan wasa a duniya, inda yake da mabiya fiye da miliyan 500 a shafukan sada zumunta na Facebook da Instagram da kuma Twitter.