Dan wasan baya na Manchester City Benjamin Mendy na fuskantar sabuwar tuhuma kan fyade wanda ke nuna zuwa yanzu dan wasan na fuskantar tuhume-tuhumen fyade har guda 7 ciki har da zargin cin zarafin wasu mata 5.
Tuhumar baya-bayan nan kan Mendy na nuna cewa dan wasan ya aikata laifin na fyade cikin watan Yuli yayinda wadancan tuhume-tuhumen suka faru tsakanin watan Octoba zuwa Agustan 2021.
Mendy wanda ke tsare tun cikin watan Agusta, ya bayyana gaban kotu yau laraba tare da Saha Matturie na City da shima ke fuskantar makamanciyar tuhumar gabanin dage zaman shari’ar zuwa watan Janairu.
A shekarar 2017 ne Manchester City ta sayo Mendy kan yuro miliyan 52 daga Monaco wanda kuma ya nuna matukar bajinta a kakar da ta gabata amma kuma zarge-zargen cin zarafin mata ya bata masa rawa da tsalle.
A wani labarin na daban Hukumar kwallon kafar Ingila ta ce ‘yan kallo ba za su halarci filin wasan da za a fafata tsakanin Arsenal da Southampton a ranar Laraba ba.
A halin yanzu hukumomin na Birtaniya sun ce dukkanin kungiyoyin dake ciki da kewayen birnin London za su rika buga wasanninsu ne ba tare da ‘yan kallo ba har sai abinda hali ya yi.
Makwanni biyu da suka gabata ne dai, hukumomin Birtaniya suka sake baiwa ‘yan kallo damar shiga filayen wasa bayan tsawon lokaci ana buga wasanni ba tare da sun baiwa idanunsu abinci kai tsaye ba, domin dakile yaduwar annobar coronavirus, koda yake ba kamar yadda aka sab aba, an takaita adadin ‘yan kallon ne zuwa dubu 2, domin kiyaye dokar baiwa juna tazara.