MDD Za Ta Yi Wani Taron Gaggawa Game Da Rikicin Rasha Da Ukraine.
A wani lokaci yau Litini ne ake sa ran Majalisar Dinkin Duniya, za ta yi wani babban taron gaggawa game da batun rikicin Rasha da Ukraine.
Taron dai na zuwa ne yayin da aka shiga kwana na biyar na matakin sojin da Rasha ta ce ta dauka kan kasar Ukraine.
A halin da ake ciki dai fadar shugaban Ukraine, ta ce kasar ta amince da tattaunawa da Rasha ba tare da wani sharadi ba, a bakin iyakarta da Belarus kusa da Tchernobyl, bayan shiga tsakani na shugaba Alexandre Loukachenko.
Jiya Lahadi, Shugaban Rasha Vladimir Putin ya bukaci manyan kwamandojin tsaron kasar da su sanya jami’an kula da makamin nukiliyar kasar cikin shirin ko ta kwana, bayan ya zargi kasashen Yammacin duniya da daukar matakan nuna kyamar kasarsa.
Putin ya ce ya shaida wa ministan tsaron kasar da babban Hafsa mai kula da rundunonin sojin kasar da su sanya dakarun da ke kula da makaman nukiliyar cikin shirin yaki.
Saidai Amurka da kawayanta sun bayyana jin takaici game da wannan matakin wanda suka ce yana da tada hankali duba da halin da ake ciki.
Alkalumman wucin gadi na bayan bayan nan da ma’aikatar kiwon lafiya a Ukraine ta fitar jiya Lahadi sun nuna cewa fararen hula 352 suka mutun tun bayan soma rikicin kana kuma 1684 suka jikkata.
Ana kuma fargabar rikicin zai haifar da gudun hijira ta mutum sama da miliyan bakwai.