MDD Ta Yi Tir Da Zartar Da Hukuncin Kisa Da Saudiyya Ta Yi Wa Wasu Mutane 81.
Kamfanin Dillancin Labarun Faransa ya nakalto shugabar kungiyar kare hakkin bil’adama ta MDD, Michelle Bachelet tana yin Allah wadai da kashe mutane 81 da Saudiyyar ta yi a ranar Asabar din da ta gabata.
Mutane 41 daga cikin jumillar wadanda aka zartarwa da hukuncin kisan dai ‘yan shi’ar kasar ne ta Saudiyya, bisa fakewa da dalilin cewa sun yi Zanga-zangar neman hakkokinsu a tsakanin shekarun 1011 da 2012.
READ MORE : Sojojin Isra’ila Sun Kashe Falasdinawa Biyu.
Shugabar hukumar kare hakkin dan’adam din ta MDD ta ci gaba da cewa; Rahotannin da mu ke da su, sun tabbatar da cewa; Shari’ar da aka yi wa mutanen da aka yanke musu hukuncin kisa ba ta cika sharuddan samar da adalci ba kamar yadda tsarin kasa da kasa ya tanada.