MDD Ta Yaba Da Kokarin Kasar Iran A Bangaren Kyautatawa Yan Gudun Hijira.
Moho Koshoor shugaban ofishin MDD dake birnin Mashad na arewa maso gabacin kasar Iran ya yabawa gwamnatin kasar Iran dangane da khidimar da takewa yan gudun hijira wadanda suek samun mafaka a kasar.
Koshoor ya kara da cewa tallafin da gwamnatin kasar Iran take bawa yan gudun hijira a bangarorin kiwon lafiya, abinci da makartu ya kai matsayin da za’a gude mata sosai kan hakan.
READ MORE : Iran; Samar Huldar Jakadanci Tsakanin HKI Da Kasashen Yankin Ba Zai Kawo Zaman Lafiya Ba.
Kamfanin dillancin labarab IP ya nakalto Koshoor yana cewa kasar Iran tana kula da ‘yan gudun hijiran Afganistan tun shekaru fiye da 40 da suka gabata, sannan yawansu na karu a ko wani lokaci, har sai da kai adadin yan gudun hijiran Afganistan ya kai mafi koli a shekarar da ta gabata bayan da Taliban ta kwace iko da kasar Afganistan a karo na biyu.
READ MORE : Falasdinu; Yara 15 Ne Sojojin Isra’ila Suka Kashe Daga Farkon Wannan Shekarar.
READ MORE : H.K.Isra’ila Ta Fara Mallakawa Yahudawa Yankunan Da Suke Daura Da Masallacin Aksa.
READ MORE : Falasdinawa Suna Da Karfin Harba Makamai Masu Linzami 150 Cikin Mintuna Biyar.