Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ta nuna damuwa dangane da yadda matsalar tsaro ke kara tabarbarewa a yankin Diffa da ke kudu maso gabashin jamhuriyar Nijar dake kusa da kan iya Najeriya, inda kungiyoyin masu ikirarin jihadi ke ta kai munanan hare-hare tun daga shekarar 2015.
Cikin sanarwa da Hukumar agaji ta Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ta fitar jiya Jumma’a tace, tsakanin watan Janairu zuwa Yunin da muke ciki, ankai hare-hare har sau tara cibiyoyin jami’an tsaro, masamman a Diffa da Maine -Soroa da Bosso, lamarin da tattabatar tabarbarewar al’amaru a tsawon iyakar kasar da Najeriya.
Ocha tace harin baya-bayan nan da aka kai ranar 5 ga watan Yuni da aka kai sansanin soji na SONIDEP kamfanin man fetur dake gabashin garin Diffa, ya raunata Jandarma daya, kafin maharani su yi awon gaba da motoci biyu bayan kone wasu.
A wani labarin mai kama da wannan Dakarun Jamhuriyar Nijar sun fafata da mayakan Boko Haram da suka kai hari kan garin Diffa dake yankin kudu maso gabashin kasar.
Mazuna yankin sun shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, mayakan na Boko Haram sun kadamar da farmaki kan garin na Diffa ne da misalin karfe 3 zuwa 4 na yammacin ranar Juma’a. Sai dai babu karin bayani kan wadanda suka rasa ransu da kuma wadanda suka jikkata, yayin fafatawar da suka yi da sojojin Nijar.
Tun shekarar 2015 yankin Diffa ke fuskantar jerin hare-haren mayakan Boko Haram, inda a watan Mayun 2020, kazamin fada ya barke tsakanin sojojin Nijar da mayakan na Boko Haram a kusa da babbar gadar Doutchi da ta sada Jamhuriyar ta Nijar da Najeriya.
Zuwa yanzu mutane kimanin dubu 300 ne ke zaman gudun hijira a yankin na Diffa, bayan da rikicin na Boko Haram ya tilasta musu tserewa daga muhallansu a Najeriya da ma wasu kauyukan kasar ta Nijar.