Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ta bukaci ilahirin hukumomin kasashe da su bada hadin kai wajen dakile shigar makamai cikin kasar Myanmar, a cigaba da daukar matakin ladaftar da gwamnatin sojojin da ta yiwa tsohuwar shugaba Aung san Su Kyii juyin mulki a farkon watan fabarairun da ya gabata.
Kasashe 119 dake zauren majalisar dinkin duniyar ne suka amince da daukar matakin, 36 suka kaurace a yayin da Belarus ta hau kujerar naki.
A makon da ya gabata shugabar hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya(MDD) Michelle Bachelet ta yi gargadin cewar tashe-tashen hankula na karuwa a sassan kasar Myanmar, tare da caccakar sojojin kasar da suka yi juyin mulki kan laifukan take hakkin dan adam da suke yi da sunan murkushe masu zanga-zangar adawa da su.
Cikin sanarwar da ta fitar Michelle Bachelete ta ce rahotannin da suka tattara sun nuna cewar rikici tsakanin kungiyoyin sa kai da jami’an tsaron Myanmar na cigaba da yin kamari a jihohin Kayah, Chin da Kachin.
A wani labarin na daban mai kama da wannan kuma majalisar Dinkin Duniya (MDD) ta bayyana cewa, rikici na tsananta a sassan Myanmar, yayin da ta yi gargadin cewa, kasar ta tsunduma cikin bala’in keta hakkin bil’adama tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a ranar 1 ga watan Fabairu.
A yayin da take mayar da martani kan yadda sojojin Myanmar suka mamaye sassan kasar, Shugabar Hukumar Kare Hakkin Bil’adama ta Majalisar Dinkin Duniya Michelle Bachelet ta bukaci gaggauta dakatar da rikicin kasar domin hana salwantar rayuka.
A cikin sanarwar da ta fitar, Bachelet ta ce, a cikin watanni hudu kacal, Myanmar ta sauya daga tafarkin demokuradiya zuwa yanayi na ibtila’in keta hakkin dan adam.
Jami’ar ta Majalisar Dinkin Duniya ta dora laifin rikicin kasar kan sojojin da suka kwace ragamar shugabancin kasar daga halastacciyar gwamnati.
Tun ranar 1 ga watan Fabairun da ya gabata ne, Myanmar ta tsunduma cikin rikici bayan janar-janar na soji sun kifar da gwamnatin Aung San Suu Kyi.
Majalisar Dinkin Duniyar ta yi laka’ri da wani sahihin rahoto da ke nuna cewa, akalla fararen hula 860 aka kashe a sanadiyar murkushewar da sojoi suka yi wa masu zanga-zangar adawa da juyin mulkin.