MDD Ta Bukaci Masana Su Samar Da Sabbin Alluran Riga Kafin Cutar Covid 19.
Hukumr lafiya ta duniya WHO ta bukaci kwararru a harkar samar da alluran riga kafin cutar Covid 19 su samar da wata allura wacce tafi inganci daga wadanda ake amfani da su a duniya a halin yanzu, sannan ta zama wacce bata da wahalarda ga wadanda suka yi ta.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ta bayyana cewa a makon da ya gabata kadai mutanen miliyon 3 ne suka harbu da cutar da covid 19 samfurin Omicron a kasashe 53 na nahiyar Turai, sannan mutane kimani 3000 ne suka rasa rayukansu sanadiyyar harbuwa da ita.
Hukumar ta bukaci masan su samar da alluran riga kafin cutar wacce zata kare mutane daga kamuwa da cutar sannan zata kashe kyayoyin cutar a cikin wadanasu suka yi alluran. Ta ci a halin yanzu dai kashi 70% na alluran bata da wannan kariyar ta kashe kwayoyin cuta.
READ MORE : 2023: Amurka tayi Hasashen Abin da zai Faru da Atiku, Tinubu, Obi, Kwankwas.
Har yanzun dai WHO ta na ganin babu wata hanya ta samun kariya daga cutar in banda yin allura da daka sanya takunkuman baki da kuma kula da tsabta.