MDD Ta Bukaci A Dauki Matakan Magance Rikicin Sudan.
Ofishin ayyukan MDD dake kasar Sudan, ya bukaci hukumomin kasar Sudan da su yi aiki tukuru domin dakile tashe-tashen hankula a dukkan sassan kasar, kana su yi kokarin maido da zaman lafiyar yankin Darfur na kasar.
Shirin MDD dake tallafawa Sudan wato (UNITAMS), ya bayyana damuwa game da karuwar tashe-tashen hankula na baya bayan nan a yankin Darfur, wanda ya yi sanadiyyar hasarar gomman rayukan fararen hula, da mutuwar masu zanga-zanga biyu a babban birnin kasar Khartoum.
Tun da farko, kafafen yada labaran cikin gidan kasar, sun bayyana cewa, fadan kabilanci da ya barke a ranar Alhamis a yankin Jebel Moon a jahar Darfur ta yammacin kasar Sudan, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 17.
READ MORE : An Kai Harin Makamai Masu Linzami A Birnin Erbil Na Iraqi.