Babban Magatakardar Majalisar Dinkin Duniya (MDD) Antonio Guterres yace Mali na iya rugujewa idan Majalisar ta janye dakarun ta dake aikin samar da zaman lafiya a cikin kasar, amma ya bada shawarar maye gurbin su da dakarun kungiyar kasashen Afirka.
Babban Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniyar (MDD) ya yi wannan bayani ne yayin zantawarsa da gidan radion Faransa International RFI dangane da yadda lamura zasu kasance game da zaman lafiya a Mali.
A taron hukamar zaman lafiyar Majalisar ta MDD da zai gudana a watan gobe ne za a samu alkiblar sabunta shirin sojojin gamaiyar hadin gwiwar wacce ke daya daga cikin muhimman shirin majalisar a fagen yaki da masu ikrarin jihadi a yankin sahel.
Gutteres ya cigaba da cewa gaskiya lamari itace rashin dakarun kiyaye zaman lafiyar na iya haifar da babbar matsala a fafutukar da ake yi ta fatattakar Yan ta’adda da kuma wahalar tabbatar da zaman lafiya, ya kuma yi wannan bayani ne cikin wata zanta wa da akayi da shi a ranar laraba data gabata.
Ya kara da cewa MINUSMA na kokari ne wajen tabbatar da samun dai daito da kuma zaman lafiya a dukkanin fafatikar da take yi ayankin na sahel mai fama da Yan ta’adda masu ikrarin jihadi.
A wani labarin na daban kuma Akalla Mutane 18 aka tabbatar da mutuwar su sakamakon wani hadarin kwale kwale a Jihar Katsina dake Najeriya, yayin da wasu kuma suka bata.
Sakatare yace 14 daga cikin su sun fito ne daga kauyen Tsabu, 4 daga Dogon Hawa, kuma tuni akayi janaizar 15 daga ciki su a Mai’adua.