MDD; Kwamitin Tsaro Ya Ki Amincewa Da Shawarar Rasha Ta Tsagaita Bude Wuta A Ukrain.
Kwamitin tsaro na MDD a jiya Laraba ya ki amincewa da bukatar kasar Rasha ta tsagauita budewa juna wuta a yakin da take fafatawa da sojojin kasar Ukrain. Yakin da ta fara tun ranar 24 ga watan Fabrairun da ya gabata.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya bayyana cewa kasashen Rasha da China ne kadai suka amince da bukatar, a yayinda sauran kasashe 10 da kuma Amurka, Burtaniya da Faransa kuma suka yi watsa da bukatar.
READ MORE : Majaliasar Dattawan Najeriya Zata Daukaka Kara Kan Hukuncin Kotun Abia Dangne Da ‘Yan Takarar Zabe.
Wannan na faruwa ne a dai-dai lokacinda makamai daga kasashen yamma suke kara kwarar zuwa kasar Ukrain don tallafawa sojojin kasar. Gwamnatin kasar Ukrain dai ta bayyana anniyar ta a fili na cewa tana bukatar shiga cikin kungiyar tsaro ta NATO, wanda kasar Rasha ke cewa hakan wata babbar barazana ce ga tsaronta.