Matashin dan wasan gaba na Faransa da ke taka leda da PSG, Kylian Mbappe ya bayayan cewa yana kishirwar ganinsa a wani muhalli daban sabanin inda ya ke yanzu, kalaman da kai tsaye ke fayyacewa yiwuwar aski ya zo gaban goshi game da shirye-shiryen sauya shekarsa.
A cewar Mbappe ya na fatan fuskantar sabon kalubale nan gaba kadan, haka zalika a kage ya ke ya hadu da sabbin abokanan wasa.
Dan wasan ya bayyana cewa fuskantar sabon kalubale a rayuwa ya fi masa muhimmanci fiye da tara dimbin dukiya a PSG.
A wani labarin na daban kuma an wasan gaba na PSG da Faransa Kylian Mbappe ya ci wa Paris Saint-Germain kwallo 100 a gasar Ligue 1, a wasan gasar na Faransa da suka doke Monaco da ci 2-0 a filin Parc des Princes ranar Lahadi.
Dan wasan na Faransa, wanda yanzu ne ya cika shekaru 23 a farkon wannan wata, ya ci wa Monaco kwallaye 16 a gasar lig a farkon kafin rabuwa da kungiyar.
Nasarar ta bai wa PSG damar kara tazarar maki 13 a teburin Ligue 1 da maki 13 gaban Marseille, wadda itama ta samu nasara a kan Strasbourg da ci 2-0 a ranar Lahadin da ta wuce kuma tana da wasa a hannunta.