Mazauna kanada sun bukaci shugaban addinin kiristanci fafaroma jamfol daya nemi gafarar su bisa abinda ya na take hakkin dan adam gami da keta hakkin mata a wata makarantar katolika wasu shekaru da suka gabata.
Mazauna kuma ‘yan asalin kanadan sun bukaci hakan ne a wani zama da akayi na awa daya ranar litinin inda suka bukaci lallai a shirya taro na musamman kuma shugaban addinin kiristancin kuma fafaroman ya bayyana sa’annan ya nemi afuwar su bisa wannan ta’asa data faru tarihi.
Kiran da mazauna na asalin kanadan ne ya sanya akayi zaman tsakanin fafaroman da kuma asalin mazauna kanadan inda fafaroma ya nemi afuwar mazaunan na kanada.
A banagare guda kuma suka bukaci fafaroman ya basu damar bincikar dukkan rubutun ajiya na babbar cocin katolikan domin tabbatar da abinda ya farua ‘yan uwan su a shekarun da suka gabata.
”Zaman yayi dadi kuma an cimma batutuwa da dama nmasu muhiommanci” kamar yadda Cassidy Caron shuagaban kungiyar asalin mazauna kanadan, kuma ya tabbatarwa da manema labarai cewa fafaroma ya saurari uku daga cikin wadanda lamarin ya rutsa dasu kuma suka samu tsira a lamarin wanda ya faru tsakanin shekarar 1831 da 1996.
Ya maimaita kalmomin gaskiya adalchi da kuma yafiya a kalaman sa kuma ya nuna alamun nadama bisa lamarin, na kuma yadda da jawaban sa domin mun hada abubuwa da yawa dashi dangaen da lamarin kamar yadda Cassidy Caron ya tabbatarwa da manema labarai.
Kamar dai yadda rahotanni suka tabbatar a kalla indiyawan metis 150,000 ne aka sanya a kusan makarantu 139 daga shekarar 1800 zuwa 1900 a makarantun dake fadin kanada wanda hakan ya raba su da iyalin su na watanni.
Mafi yawancin yaran da aka dauka daga gidajen iyayen su sun gamu da matsalolin twangwama, fyade, hana abinci da kuma wulakanci wanda kuma hakan yayi sanadin mutuwar akasarin su.
Rahotanni sun tabbatar da cewa gwamnatin kanada ta nemi afuwa sakamakon matsin lambar da ta samu a shekarar 2008.